
Damisa ta kamu da Coronavirus a Amurka
Monday, 6 April 2020
Comment
Gwajin da aka yi kan wata damisa 'yar shekara hudu a gidan namun dajin Bronx Zoo da ke Amurka ya nuna cewa ta kamu da coronavirus.
An yi amannar cewa damisar, wacce ake kira Nadia, ita ce dabba ta farko da ta kamu da Covid-19 a Amurka.
Mahukuntan gidan namun daji na Bronx Zoo, wanda ke birnin New York City, dakin gwaji na kasa na gandun dabbobi da ke Iowa ne ya tabbatar da cewa damisar na dauke da cutar.
An yi amannar cewa wani ma'akacin gidan namun daji ne ya shafa wa Nadia da wasu dabbobi dangin damisa su shida, coronavirus.
Dabbobin sun soma nuna alamun kamuwa da coronavirus, ciki har da yin tari mara majina, a watan jiya bayan sun yi mu'amala da mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba.
''Wannan ne karo na farko da aka samu irin wannan labarin a duniya cewa wani mutum mai dauke da cutar ya shafa wa dabba har ma ta fara da rashin lafiyar,'' kamar yadda Paul Calle babban ai kula da gidan Zoo din ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Lahadi.
An samu labaran yadda a wasu sassan duniya da aka samu dabbobin da suka kamu da cutar, amma kwararru sun yi gargadi cewa babu wata hujja da ke tabbatar da cewa za su iya yin rashin lafiya ko su yada cutar.
Mr Calle ya ce ya yi niyyar ya fitar da bayanan bincikensa ya rarrabawa sauran gidajen adana namun daji da cibiyoyin da ke bincike kan yaduwar Covid-19.
"Mun yi wa damisa [Nadia] gwaji kuma za mu tabbatar da cewa duk wani ilimi da muka samu a kan Covid-19 zai taimaka wa duniya wajen sake gano yadda cutar take,'' kamar yadda sanarwar gidan zoo din ta fada.
Ana sa ran Nadia da 'yar uwarta Azul, da kuma wasu damussan biyu da zakunan AFirka da suka nuna alamun cutar, za su warke tas, a cewar gidan zoo din.
''Dabbobin suna fama da rashin son cin abinci amma in ban da haka suna nan lafiya karkashin kulawar likitan dabbobi,'' in ji sanarwar.
Gidan zoo din ya ce ba a san ta yaya kwayar cutar ke yaduwa a jikin dabbobi kamar damusa da zakuna ba, tun da dabi''ar kowace dabba ta bambanta yayin da suka kamu da sabuwar cuta, amma za a sa ido kan dukkan dabbobin.
Babu daya daga cikin dabbobin da suka hada da damisa da zakunan yankuna daban-daban da ke nuna alamar wata rashin lafiya.
Me muka sani game da dabbobi da cutar?
A bara ne aka fara gano wannan kwayar cuta a jikin 'yan adam a birnin Wuhan na China.
An yi amannar kwayar cutar mai suna (Sars-CoV-2, wacce take haddasa Covid-19) ta samo asali ne daga jikin dabobin daji ta yadu zuwa ga 'yan adam a wata kasuwar dabbobi a Wuhan.
Annobar dai tana yaduwa ne daga mutum zuwa mutum, amma a yanzu da ta kama damisa NAdia ta dasa alamomin tambaya kan yaduwar cutar daga dan adam zuwa dabbobi.
Sai dai ba a samu rahotonni da yawa kan bullar cutar a jikin dabbobi ba, amma an samu kadan kamar na Nadia da wasu karnuka biyu a Hong Kong.
Sanarwar gidan zoo din ta ce ba a samu dabbobin da suka kamu da cutar ba a Amurka ko da kuwa dabbobin gida kamar mage da kare.
Haka ma Kungiyar Lafiyar Dabbobi Ta Duniya da Hukuar LAfiya ta WHO sun ce babu wata hujja da ke nuna cewa karnuka da maguna za su iya yada coronavirus.
KARANTA: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa
DAGA MUJALLAR:https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Damisa ta kamu da Coronavirus a Amurka"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?