
Dalilin da ya sa ban hana zirga-zirga a Jihar Kuros-Riba ba – Inji Ben Ayade
Tuesday, 14 April 2020
Comment
Ben Ayade ya na ganin cewa kare rayukan jama’a ba tare da kare hanyar samun abincinsu ba zai iya jefa kasar cikin wata sabuwar matsala dabam bayan annobar cutar Coronavirus. “Wasu ‘Yanuwanmu Maza da Mata sun dogara ne da fita kwadago kullum domin su samu abinci. Idan ka na daukar kankare ne a duk ranar Duniya, a ranar da aka hana ka zuwa aiki, ba za ka samu kudin da za ka ciyar da ‘Ya ‘yanka ba.” Inji Mai girma Gwamna Ayade.
A dalilin haka, gwamnan ya ce ya na adawa da rufe jihar, ya ce gara a kyale mutane su cigaba da harkokin gabansu su nemi kudi muddin sun rufe fuskarsu da tsummar kariya.
Ayade ya na jin tausayin wanda sai ya fita zai samu hanyar ci da Iyalinsa Source: Twitter
Ayade ya yi wani karin bayani: “A fadin Duniya, yunuwa da makamantan cututtukanta irinsu Kwashiorkor da Tarin TB su kan kashe mutane kusan miliyan 8.4 a duk shekara.” Don haka ne gwamnan ya ke ganin cewa babu wata annoba da ta fi yunwa a Duniya. “Za mu yi duk abin da za mu iya na takaita yaduwar wannan annoba a cikin jiharmu.”
“Za kuma mu kare rayukan Jama’a, amma kuma akwai tangarda wajen kare rai ba tare da an tsare hanyar da za ta samu abinci ba. Dole a samu kyakkyawar alaka tsakaninsu.” Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan ya yi wannan jawabi ne ga Manema labarai a Ranar Litinin a Garin Kalaba. Gwamna Ayade ya fi maida hankali ga amfani da tsummar rufe fuska.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Dalilin da ya sa ban hana zirga-zirga a Jihar Kuros-Riba ba – Inji Ben Ayade "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?