--
Dakarun MNJTF sun halaka mayakan Boko Haram 19 a Tumbum

Dakarun MNJTF sun halaka mayakan Boko Haram 19 a Tumbum



- Rundunar jami'an tsaro ta hadin gwiwa (MNJTF) ta kai samame ga mayakan Boko Haram a Tumbum da ke yankin iyaka na tsibirin Chadi - Rundunar dai ta hada da dakaru ne daga Najeriya, Chadi, jamhuriyar Nijar da kuma kasar Kamaru

- A harin da suka kai wa 'yan ta'addan ta jiragen yaki da kuma ta kasa, sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram 19 tare da kwace motocin yaki biyu Rundunar jami'an tsaro ta hadin gwiwa wacce ta hada da jami'an tsaron kasashen Najeriya, Chadi,

jamhuriyar Nijar da Kamaru sun halaka a kalla 'yan ta'addan Boko Haram 19 a tsibirin tafkin Chadi kusa da yankin iyakokin da ake kira da Tumbum, jaridar The Nation ta ruwaito. Rundunar jami'an tsaron ta hadin guiwa a ranar Litinin ta ce rundunar Operation Yancin Tafki ce ta kai wa 'yan ta'addan hari ta jiragen yaki na sama. Wasu daga cikin jami'an tsaron kuwa sun je ta kasa ne ta inda suka far wa mayakan a maboyarsu.

Jami'in yada labarai na rundunar hadin guiwar Kanal Timothy Antigha ne ya sanar da hakan a takardar da ya fitar. Ya ce rundunar ta tarwatsa mayakan ta'addancin ta jiragen sama na yaki da kuma ta kasa inda suka kwace motocin yaki biyu. Ya ce: "Daga cikin yaki da ta'addancin da rundunar hadin guiwa take yi karkashin Operation Yancin Tafki,

jami'an tsaro daga Najeriya, jamhuriyar Nijar da kuma Kamaru sun tarwatsa maboyar 'yan ta'adda a Tumbum da safiyar Litinin." Ya kara da cewa, "A wannan karon, jiragen sama na yaki da kuma dakaru ta kasa ne suka kai samamen. An halaka mayaka 19 na Boko Haram inda wasu suka tsere.

Rundunar hadin guiwar tare da taimakon sojin sama sun tarwatsa motocin yakin 'yan ta'addan biyu sannan suka samu kwace biyu." "Babura hudu da wasu miyagun makamai duk an kwace. Babu ko mutum daya da ya samu rauni a rundunar hadin guiwa ta jami'an tsaron. Wannan kokarin ana sa ran zai murkushe tare da rage karfin mayakan ta'addancin na Boko Haram. Hakan kuma na jaddada nasarar rundunar hadin guiwar wajen a cikin yankunan da aka basu don yaki da ta'addancin," Ya kara da cewa.
KARANTA: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

DAGA MUJALLAR:https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Dakarun MNJTF sun halaka mayakan Boko Haram 19 a Tumbum "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?