
Da Dumi-Dumin sa: Sarkin Saudiyya ya bada umarnin rabawa 'yan kasar Riyal biliyan 9
Friday, 3 April 2020
Comment
Sarki Salman Bin Abdulaziz na Saudiyya ya bada umarnin a rabawa 'yan kasar dama wanda suke zaune a kasa bisa sola zunzurutun kudi kimanin Riyal biliyan Tara, kwatankwacin Naira biliyan 900 domin saukaka musu daga radadin halin da suke ciki.
Saudiyya dai na daya daga cikin kasar da cutar corona virus tayiwa mugun kamu a kasashen yankin gabas ta tsakiya, inda aka samu cutar a jikin mutane sama da mutum 2500.
Wani dan Najeriya mazaunin kasar wanda ya shaida mana cewar yana zaune a kasa tare da mallakar dukkan takardun zama yace an bashi kimanin kudin Najeriya Naira 275,000 daga cikin wadancan kudade da Sarki Salman ya bada umarnin rabawa 'yan kasa.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
0 Response to "Da Dumi-Dumin sa: Sarkin Saudiyya ya bada umarnin rabawa 'yan kasar Riyal biliyan 9"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?