--
COVID-19: Za mu gwada amfani da magungunan gargajiya - Ministan lafiyal

COVID-19: Za mu gwada amfani da magungunan gargajiya - Ministan lafiyal

- Ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce gwamnatin tarayya za ta fara duba masu ruwa da tsaki a fannin magungunan gargajiya don yakar cutar coronavirus a kasar nan

- Ministan ya sanar da hakan ne a taron manema labarai da yayi tare da kwamitin shugaban kasar na yaki da cutar coronavirus wanda aka yi a Legas a ranar Talata 

- Ministan ya ce gwamnatin tarayya tana kara dogaro ne da cibiyar kiwon lafiya ta duniya kamar dai yadda sauran kasashe ke yi don gano ingantaccen maganin muguwar cutar Ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce gwamnatin tarayya za ta fara duba masu ruwa da tsaki a fannin magungunan gargajiya don yakar cutar coronavirus a kasar nan. 


Ministan ya sanar da hakan ne a taron manema labarai da yayi tare da kwamitin shugaban kasar na yaki da cutar coronavirus wanda aka yi a Legas a ranar Talata. Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, ya ce za a duba a ga manyan masu maganin gargajiya da ke amfani da tsumi, sassake da dauri don gwaji. 

COVID-19: Za mu gwada amfani da magungunan gargajiya - Ministan lafiya Source: UGC 

"Za mu duba ta kowanne bangare ne da niyyar samun mafita. Wasu suna cewa suna da maganin gargajiya da zai kashe cutar. Wadanda suka mayar da hankali kadai ma'aikatar lafiya za ta saurari ikirarinsu kuma ba za mu gwasale su ba," 

yace. "Za mu duba ingancin magungunan gargajiyan kafin mu aminta da shi don amfanin jama'a." Ya ce. Ya kara da cewa, za a yi gwaji mai tarin yawa kafin a a tabbatar da maganin sannan a fitar. 

"Kamar abinda ya faru da hydroxychloroquine wanda aka samu yana aiki a waje amma ba a jikin dan Adam ba. Dole ne kuwa a tantance magungunan gargajiya da kuma gano illolinsu," yace. Ministan ya ce gwamnatin tarayya tana kara dogaro ne da cibiyar kiwon lafiya ta duniya kamar dai yadda sauran kasashe ke yi don gano ingantaccen maganin muguwar cutar.  KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: Za mu gwada amfani da magungunan gargajiya - Ministan lafiyal"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?