--
COVID-19: 'Yan fashi da makami sun balle shaguna a Legas

COVID-19: 'Yan fashi da makami sun balle shaguna a Legas


- Wasu da ake zaton 'yan daba ne sun balle shaguna da wasu gidaje a yankin Alimosho a jihar Legas a ranar Asabar - An gano cewa 'yan daban sun je yankin ne daga yankin Agbado inda suka fasa shagunan tare da yi wa mazauna yankin fashi

- Wani mazaunin Abule Egba, ya ce matasan yankin sun yi kokarin hana barnar tare da kwace wasu kayayyakin da aka sace Wasu da ake zaton 'yan daba ne sun balle shaguna da wasu gidaje a yankin Alimosho a jihar Legas a ranar Asabar. An gano cewa 'yan daban sun je yankin ne daga yankin Agbado inda suka fasa shagunan tare da yi wa mazauna yankin fashi.
Kamar yadda jaridar The Cable ta bayyana, wasu ganau ba jiyau ba sun ce lamarin ya faru ne da ranar Allah. 'Yan daban kuwa sun kwashe kayayyakin abinci ne. "Sun iso ne a motoci kirar bas guda uku, sun dinga harbi a iska kafin su fara kwasar kayan," daya daga cikin mazauna yankin Agbado ya sanar. Kamar yace, "Masu shagunan sun dinga gudu don tseratar da rayukansu. Sun kai hari wasu gidaje tare da yi musu fashin kudi da kayayyakin amfani."

Wani mazaunin Abule Egba, ya ce matasan yankin sun yi kokarin hana barnar tare da kwace wasu kayayyakin da aka sace. "Matasan sun fito da yawansu inda suka fuskanci 'yan fashin kafin 'yan sanda su iso, " tace. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar The Cable. Ya ce an damke wasu daga cikin wadanda ake zargi. "Yan daban sun fito duk da cewa basu da damar fitowa saboda kullen. Mun datsesu don jami'an mu a shirye suke",
yace. A cewarsa, "Sun fara da harar junansu don jama'a su taru. Daga nan suka yi amfani da damar wajen sata. Muna da jami'ai a wajen don haka suka yi martanin gaggawa. Mun kama da yawa daga cikinsu". KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: 'Yan fashi da makami sun balle shaguna a Legas"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?