
COVID-19 ta fara yaduwa tsakanin junan ‘Yan Najeriya – Minista
Tuesday, 7 April 2020
Comment
Ministan lafiya watau Dr. Osagie Ehanire ya nuna wannan alamu tun a makon da ya gabata. Ganin yadda ake samun karuwar cutar, Ministan ya ce ta na yawo tsakanin ‘yan kasa. Ministan na Najeriya, Osagie Ehanire, ya fara yin wannan bayani lokacin da ya ke wani jawabi a lokacin da aka gayyace shi a gidan talabijin na TVC a Ranar Alhamis da ta gabata. Ehanire ya ke cewa mutane su na kamuwa da wanan cuta ba tare da sun fita Najeriya ba, sai da ta hanyar haduwa da wani da ba a san cewa ya na dauke da kwayar cutar a jikinsa ba.
Bayan an samu masu dauke da kwayar cutar COVID-19 a Osun da Ekiti, maganar yaduwar cutar tsakanin ‘Yan kasa ta kara karfi. Wannan ya sa aka kara kiran a rage shiga Jama’a. Kwamishinan lafiyan jihar Legas, Dr, Akin Abayomi, ya tabbatarwa ‘Yan jarida wannan kwanaki a lokacin da su ka zanta, ya ce babu shakka cutar ta na yawo a cikin gida a Legas.
Su ma Likitocin Najeriya sun bayyana cewa wannan cuta mai kawo wahalar numfashi ta na yawo tsakanin mutanen gida bayan ganin yadda cutar ta ke kara yaduwa a kasar. Kamar yadda BBC Hausa ta bayyana, Likitocin kasar a karkashin kungiyarsu ta NMA, sun nuna rashin goyon bayan gayyatar da Najeriya ta yi wa Malaman asibiti daga kasar Sin.
KARANTA: Damisa ta kamu da Coronavirus a Amurka Karanta Anan
DAGA MUJALLAR:https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "COVID-19 ta fara yaduwa tsakanin junan ‘Yan Najeriya – Minista"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?