
Covid-19: Sauyawar sakamakon gwaji a UBTH ya jefa tsoro a zukatan ma'aikata da jama'a
Sunday, 5 April 2020
Comment
- Ma'aikatan lafiya da jama'a a Benin sun shiga halin firgici bayan wasu an samu kwayar cutar covid-19 a jikin wasu mutane da sakamakon gwajin farko ya nuna cewa basa dauke da kwayar cutar
- Daya daga cikin mutanen yana daga cikin masu dauke da cutar covid-19 da ake zargin cutar ta kashe Najeriya - Bincike ya nuna cewa mai dauke da kwayar da ya mutu a UBTH, yana fama da matsanancin ciwon koda An samu rudani da firgici a cibiyar gudanar da gwaji da killace masu dauke da kwayar cutar covid-19 da ke asibitin koyarwa na jami'ar Benin (UBTH) sakamakon sauyawar sakamakon gwajin wasu masu dauke da kwayar cutar coronavirus.
A ranar juma'a ne cibiyar shawo kan cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da cewa wasu mutane biyu da ke dauke da kwayar cutar covid-19; daya a Legas, daya a Benin, sun mutu ba tare da bayar da karin bayani ba, lamarin da ya saka jama'a cikin fargaba a Benin.
Jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa sakamakon gwajin farko da aka gudanar a kan wasu mutane ya nuna cewa basa dauke da kwayar da cutar, amma sakamakon gwajin da aka maimaita ya nuna cewa suna dauke da kwayar cutar.
Tun bayan gwajin farko daka gudanar a kan mutanen, kungiyar likitocin asibitin (NARD) ta bayar da shawarar a mayar da su cibiyar killacewa a ranar 31 ga watan Maris, bisa zargin cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19.
Babban darektan likitocin asibitin UBTH, Farfesa Darlington Obaseki, ya bukaci jama'a su kwantar da hankalinsu tare da basu tabbacin cewa babu abinda zai gagari likitocin a kokarinsu da shawo kan annobar cutar. A jawabin da hukumar asibitin ta fitar, ta bayyana cewa masu dauke da kwayar cutar da sakamakon nasu ya zo da rudani, suna fama da wasu sauran cututtukan kamar yadda sakamakon wasu gwaje-gwajen da aka yi musu ya nuna.
LATSA NAN๐๐๐ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐๐๐https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Covid-19: Sauyawar sakamakon gwaji a UBTH ya jefa tsoro a zukatan ma'aikata da jama'a "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?