--
COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)



- Tun bayan bullar annobar Covid-19 a kasashen duniya, masallatai manya na duniya sun daina sallar jam'i tare da rufe duk wasu ayyukansu - Kamar yadda kasar Saudia ta bayyana rufe manyan masallatai masu daraja guda biyu na kasar,













haka sauran manyan masallatan duniya suka yi - Amma kuma akwai msallatai da yawa har da na kasar Saudi Arabia da ake bari ana sallar jam'i amma cike da dokar nisantar juna Tun bayan barkewar annobar cutar Covid-19 a duniya ne masallatai manya suka daina sallar jam'i. Musulmai da yawa tare da gwamnatocin kasashen duniya sun dauka wannan matakin ne don hana yaduwar annobar.

Wannan haramta sallar a jam'in kuwa ya jawo cece-kuce a wurin musulman duniya. Yayin da wasu suka ki bin dokar, sun dauka matakin dakile cudanya da juna tare da nisantar juna duk da kuwa ana sallar jam'in.

A sabon salon sallar jam'in, babu batun hada kafadu ko kafafu kamar yadda jam'i yake bayyana. Ga wasu zababbun hotunan yadda ake sallar jam'i a manyan masallatai daban-daban na fadin duniya.

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmad Lawan ya bayyana sanata daga jihar Osun, Ajibola Basiru a matsayin sabon shugaban kwamitin yada labarai na majalisar. Basiru zai dasa daga inda Sanata Godiya Akwashiki ta tsaya a matsayin mukaddashin kakakin majalisar. Ta ci gaba da aiki a matsayin kakakin majalisar dattijan ne tun bayan da aka kwace kujerar Adebayo Adeyeye a kotu.

Akwashiki sanata ce a karkashin jam'iyyar APC daga jihar Nasarawa. Ba kakakin majalisar kadai zai tsaya ba, zai kasance shugaban kwamitin majalisar na daukar aiki da kwadago. Sanata Biodun Olujimi ta jihar Ekiti karkashin jam'iyyar PDP ce ta zama shugabar kwamitin majalisar mai kula da 'yan Najeriya da ke kasashen ketare da kuma kungiyoyin taimakon kai da kai. Lawan ya bada wannan sanarwar ne a yayin tashi zaman majalisar na yau Talata, jaridar Premium Times ta

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?