--
COVID-19: Rudani a Kano bayan an gano mai coronavirus ya halarci sallar Juma'a

COVID-19: Rudani a Kano bayan an gano mai coronavirus ya halarci sallar Juma'a


- Wanda aka gano yana dauke da cutar coronavirus a jihar Kano ya ziyarci a kalla wurare uku kuma akwai yuwuwar ya shafa wa wasu cutar 

- An gano cewa mutumin ya je masallacin Juma'a, ya ziyarci wani asibitin kudi da kuma kwatas din da gidan shi yake - A ranar 11 ga watan Afirilun 2020 ne jihar Kano ta samu mutum daya da ke dauke da cutar coronavirus Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya bayyana cewa mutumin da ke dauke da cutar coronavirus a jihar Kano ya je sallar Juma'a a Masallaci. 

Wannan lamarin kuwa ya jawo rudani da tsananin tashin hankali ga manyan jami'an gwamnatin jihar. Idan zamu tuna, jihar Kano din ta samu mutum na farko mai dauke da cutar a ranar Asabar, 12 ga watan Afirilu. An gano cewa an kwantar da mutumin ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke GRA Nasarawa a jihar Kano. 

Wata majiya daga asibitin ta bayyana cewa, an kwashe dukkan ma'aikata da majinyatan asibitin inda aka killacesu. 

An gano cewa, an kara da kwashe wasu masu makwabtaka da asibitin don gwaji. Majinyacin dai yana da shekaru 75 kuma tsohon jakada ne. Ya isa Kano ne daga Legas, inda ake zargin ya debo cutar. Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, kanwarsa da aka aika an hana ta shiga gidan iyalan mutumin. 

Hadiman gidan tare da iyalansa da ke kwatas din Giginyu duk an kwashe su zuwa cibiyar killacewa. Hankalin jama'a mazauna wurin ya matukar tashi bayan gano wa da aka yi cewa mutumin na dauke da cutar. Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, kwamishinan lafiya na jihar Kano, 

ya ce an tura jami'an kwamitin hana yaduwar cutar zuwa wurare uku da mutumin ya je. Wuraren da ya ziyarta kuwa sun hada da kwatas din Giginyu, masallacin Juma'a na Da'awah da kuma asibitin kudin da aka kwantar da shi.

KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: Rudani a Kano bayan an gano mai coronavirus ya halarci sallar Juma'a "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?