--
COVID-19: NECO ta karyata rade-radin cewa za ta dage jarrabawar BECE da SSCE

COVID-19: NECO ta karyata rade-radin cewa za ta dage jarrabawar BECE da SSCE



- Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) ta musanta labarin dage jarabawoyin daliban aji uku da na aji shida na sakandire - Kamar yadda shugaban fannin yada labaran hukumar ya sanar, suna lura da halin da kasar ke ciki ne kafin daukar mataki



- Hukumar ta bayyana cewa ta dage jarabawar masu kammala karatun firamare don shiga sakandire ta shekarar 2020 Hukumar jarabawa ta kasa (NECO) ta musanta rade-radin dage jarabawoyinta da ake yadawa sakamakon barkewar annobar coronavirus a kasar nan. A wata takarda da shugaban fannin yada labarai da hulda da jama'a, Malam Azeez Sani ya fitar,



ya ce hukumar ta bayyana cewa jarabawar masu kammala firamare kadai ta dage. Ya ce labarin dage jarabawoyin da suke yawo a kafafen sada zumuntar zamanin duk na bogi ne kuma ba gaskiya bane.



Ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da labaran marasa tushe balle makama. Ya ce, "Hukumar ta duba sauran jarabawoyin masu kammala aji uku da kuma aji shida na sakandare amma tana tantamar dagesu a halin yanzu." Ya kara da cewa, "Ana kira ga daukacin jama'a da su yi watsi da labaran bogin don hukumar na lura da abinda ke faruwa a kasar nan, kuma za ta sanar da matsayarta idan da bukatar hakan."



Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa NECO ta dage rubuta jarabawar kammala firamare na 2020 a ranar 24 ga watan Maris. "NECO na sanar da masu rubuta jarabawa, iyaye da kuma masu ruwa da tsaki cewa ta dage jarabawar NCEE har sai yadda hali yayi," A cewar takardar. "Wannan hukuncin ya biyo bayan kokarin gwamnatocin tarayya da na jihohi ne wajen ganin an shawo kan barkewar cutar coronavirus a kasar nan, in ji hukumar.KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: NECO ta karyata rade-radin cewa za ta dage jarrabawar BECE da SSCE "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?