
COVID-19: Ministan FCT ya sanar da kwanakin bude kasuwanni
Thursday, 16 April 2020
Comment
- Ministan babban birnin tarayya ya bayyana cewa za a fara bude kasuwannin a ranakun Laraba da Asabar - Ministan, wanda ya sanar da hakan yayin taron kwamitin tsaro na yaki da annobar, ya jajanta yadda mazauna garin ke amfani da damar zuwa kasuwa don karya doka
- Birnin tarayyar zai shirya wayar da kai ga jama'ar karkara tare da hadin guiwar shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin al'umma A kokarin ganin jama'a sun bi dokar hana zirga-zirga a babban birnin tarayya don hana yaduwar cutar coronavirus, ministan birnin tarayya ya bayyana cewa za a fara bude kasuwannin a ranakun Laraba da Asabar. Ministan ya ce kotun tafi-da-gidanka za ta fara aiki don ladabtar da masu laifi.
Ministan, wanda ya sanar da hakan yayin taron kwamitin tsaro na yaki da annobar, ya jajanta yadda mazauna garin ke amfani da damar zuwa kasuwa don karya doka. Ya ce mazauna garin basu bin dokar hana zirga-zirgar. A wata takardar da sakataren yada labarai na ministan, Anthony Ogunleye ya fitar, ya ce an rage ranakun cin kasuwanni don haka kwanaki biyu kacal za su dinga budewa.
Ana shawartar mazauna yankin da su ziyarci kasuwannin kusa dasu don an haramta zirga-zirga daga yanki zuwa yanki. "Kotun tafi-da-gidanka za ta fara aiki don hukunta dukkan masu laifi a fadin birnin tarayyar," yace. Sabbin dokokin sun haramtawa babur yawo a Kubwa da Dutsen Alhaji yayin kullen. Birnin tarayya zai shirya wayar da kai ga jama'ar karkara tare da hadin guiwar shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin al'umma.
Hakan zai sa su gane illolin muguwar cutar. A wani labari na daban, mazauna garin Daura sun bayyana cewa kullen da suke fuskanta a garin ya kara musu yunwa ne don basu da kudin siyan abinci. Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, Barista Ado Lalu mazaunin garin ne wanda yayi magana a madadin jama'ar garin. "Da yawa daga cikinsu basu shirya wa kullen ba. Babu kudi balle mu siya kayan abinci mu ajiye. Da yawa daga cikinmu wadanda ke aikin kullum sun dogara da abokai da makwabta ne don ciyarwa," yace.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "COVID-19: Ministan FCT ya sanar da kwanakin bude kasuwanni "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?