--
COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu

COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu



- Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, kwamishinoni uku da diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun killace kansu - Sun yanke shawarar killace kansu ne bayan an gano cewa mataimakin shugaban kwamitin, Farfesa Abdulrazaq Garba Habibu na dauke da cutar

- Kamar yadda hukumar kula tare da takaita yaduwar cutuka ta bayyana, da karfe 10:20 na daren Alhamis, an samu mutane 21 a jihar masu dauke da cutar Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, kwamishinoni uku da diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun killace kansu bayan an gano cewa sun yi mu'amala da wani mai cutar.

Mambobin kwamitin hana yaduwar cutar COVId-19 din wacce mataimakin gwamna Gawuna ke shugabanta, sun hada da Balaraba Ganduje, kwamishinan lafiya Aminu Tsanyawa, kwamishinan muhalli Kabiru Getso da Imam Wada, sakataren kwamitin.

COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu Source: Facebook


Jaridar Daily Trust ta gano cewa sun yanke shawarar killace kansu ne bayan an gano cewa mataimakin shugaban kwamitin, Farfesa Abdulrazaq Garba Habibu na dauke da cutar. Majiya mai karfi daga gwamnatin ta ce, "Kun san tunda tare suke aiki da mataimakin shugaban kwamitin kafin ya san yana dauke da cutar, zai fi idan sauran mambobin suka kullace kansu. "An dauka jininsu don dubawa ko suna dauke da cutar amma har yanzu ba a samu sakamakon ba.

"Muna fatan sakamakon ya nuna basu dauke da cutar. Amma ina tabbatar muku da cewa dukkan 'yan kwamitin suna killace tare da jiran sakamako," majiyar tace. Idan za mu tuna, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da kwamitin a ranar 21 ga watan Maris 2020. Alhakin takaita yaduwar annobar a jihar Kano ya hau kansu tare da duk wani kokarin zakulo masu cutar.

Kamar yadda hukumar kula tare da takaita yaduwar cutuka ta bayyana, da karfe 10:20 na daren Alhamis, an samu mutane 21 a jihar masu dauke da cutar. A yau ne dokar hana zirga-zirga da gwamnan jihar Kano ya saka ta fara aiki. An ga hotunan birnin Kano kamar an shareshi saboda jama'ar jihar sun yi biyayya ga dokar.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/





LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?