
COVID-19: Ma'aikatan Lafiya bakwai sun kamu da Korona a Borno
Friday, 24 April 2020
Comment
– Ma'aikatan Lafiya guda bakwai a jihar Borno sun kamu da kwayar cutar COVID-19 – Kwamishinan Lafiya na jihar, Kwaya-Bura ne ya bayyana hakan a ranar Jumaa a garin Maiduguri – Kwamishinan ya ce mutum 15 ne suka kamu da cutar a jihar inda biyu cikinsu sun riga mu gidan gaskiya Kwamishinan Lafiya na jihar Borno,
Salihu Kwaya Bura ya ce ma'aikatan lafiya bakwai a jihar sun kamu da kwayar cutar COVID-19 da ake fi sani da coronavirus. Kwaya-Bura wanda kuma shine sakataren kwamitin kar ta kwana na yaki da annobar Korona a jihar ya bayyana hakan ne a ranar Jumaa a Maiduguri yayin da ya ke bayar da bayani a kan annobar a jihar. Ya ce mutane 15 ne suka kamu da cutar a jihar kawo yanzu sannan mutum biyu sun mutu.
"An binciko wadanda suka yi cudanya da wandanda suka kamu da cutar kuma ana sa ido a kansu domin ganin halin da suke ciki. "Mutane sun ankarar da mu game da mutane tara da ake zargin sun kamu, mun yi bincike a kansu, bakwai cikinsu ba su da alamomin cutar amma muna cigaba da bincike a kan biyu,"
in ji Kwaya-Bura. Ya jinjinawa al'ummar jihar bisa hakuri da sadaukarwarsu a rana da biyu bayan saka dokar kullen inda ya ce kwamitin kar ka kwanan tana shirin yin sausauci ga dokar don albarkacin watan Ramadana. Kwaya-Bura ya ce, "Muna son mu ga yadda za mu bari masu sayar da kankara, kosai da shayi da biredi su fara yin sanaarsu a gundumominsu domin mutane su rika saya lokacin shan ruwa."
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "COVID-19: Ma'aikatan Lafiya bakwai sun kamu da Korona a Borno "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?