--
Covid-19: Lokacin da 'yan Najeriya za su fara faduwa suna mutuwa yana nan tafe - Farfesa Usman

Covid-19: Lokacin da 'yan Najeriya za su fara faduwa suna mutuwa yana nan tafe - Farfesa Usman



Batun kunnen uwar shegu da nuna halin 'ko in kula' da jama'a ke yi a kan sharwarar masana da biyayya ga matakan gwamnati domin kare kai daga kamuwa da cutar covid-19 ya fara saka damuwa a zukatan kwararru a harkar lafiya a Najeriya. Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa NHIS),

Farfesa Usman Yusuf, ya nuna damuwarsa tare da bayyana cewa abinda suke gani a matsayinsu na kwararru yana matukar tayar musu da hankali A cewar tsohon shugaban na NHIS, annobar cutar covid-19 za ta iya yin mummunar barna a Najeriya matukar jama'a basu yadda suke wasarairai da matakan kare kai daga kamuwa da cutar ba. A hirar da ya yi da sashen Hausa da rediyon BBC, Farfesa Usman,

hankalin likitocin Najeriya har ma da na kasashen ketare a tashe yake saboda ganin annobar cutar da ta fara daga kasar China, inda ta kashe dumbin mutane, yanzu ta bazu zuwa kowanne yanki na duniya. "Dubi yadda cutar ta yi barna a Italy, ta shiga Ingila har ta kai ga yanzu an kwantar da shugabansu a asibiti saboda yana dauke da wannan cuta.

Farfesa Usman Yusuf Source: UGC

 "Ta shiga kasar Amurka sai barna take yi duk kudinta da bama-bamanta. Mutane sai mutuwa suke yi inda ake mayar da filayen wasa asibiti. "Amma mu a nan Najeriya, jama'a basu dauki cutar da muhimmancin da ya kamata ba, hakan ya tashi hankalinmu, musamman yadda muke jin jama'a na cewa ba ta zo arewa ba, ai ba ta kawo nan ba," a cewarsa.

Sanna ya cigaba da cewa, "duk maganganun nan ba gaskiya bane, duk kasashe akwai lokacin da kwayar cutar ke bunkasa idan jama'a basu bayar da goyon ba. "Idan jama'a basu fahimta ba haka za mu cigaba da abubuwa, mutane suna faduwa suna mutuwa." Kazalika ya bayyana cewa, kar jama'a su yi kuskuren tunanin cewa iyakar mutanen da aka sanar ne kadai ke dauke da kwayar cutar. Ya kara da cewa,

"ai ba za a san iya adadin masu dauke da kwayar cutar ba sai an bincika. Mu na zama ne kawai mu na cewa ai Legas ne da Ogun kawai, shikenan sai a kwanta a cigaba da zuwa Masallaci ana yi wa juna tari, ana zuwa kasuwanni, ana shiga motocin haya, ana cigaba da cewa ai ciwon Abuja ne, ai ciwon Legas ne", wanda a cewar Farfesan, "sam hakan ba gaskiya bane".


KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Covid-19: Lokacin da 'yan Najeriya za su fara faduwa suna mutuwa yana nan tafe - Farfesa Usman "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?