
COVID-19: Lauyoyi sun yi gudun ceton rai bayan wanda ake zargi ya yi tari a kotu
Wednesday, 15 April 2020
Comment
Wannan ci gaban kuwa ya kawo tangarda a shari'ar don kuwa lauyoui uku ne suka gaggauta tserewa. Duk da faruwar wannan lamarin kuwa, mai shari'a Olusegun Ayilara ya sanar da wanda ake zargin cewa tarinsa ba zai tsayar da abinda ake yi ba.
An gurfanar da Ige ne tare da wani mai suna Rasaq Sunday, Wasiu Adeyanju da Samson Ogunleye. Ana zargin cewa a ranar 6 ga watan Afirilun 2020 a titin Olugun da ke Osogbo, sun hada kai wajen aikata laifi wanda ya ci karo da sashi na 516 na dokokin laifukan jihar Osun na 2002.
An zargesu da yin amfani da fasassun kwalabe, almakashi da adda wajen raunata wani mai suna Lateef Kareem. Rasaq Olayiwola ne ya sanar da bayyanar masu gurfanarwar. Wanda ake zargin wanda bashi da lauya, ya musanta zargin da ake masa. Alkalin kotun, Ayilara, ya bada belin wanda ake zargin a kan N200,000 da kuma tsayayye daya. Ya dage sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Maris.
A wani labari na daban, wani jinjiri a garin Saharanpur da ke Uttar Pradesh a kasar India, an sa mishi suna 'Sanitizer'. Iyayen sun ce sun yi hakan ne don tunatar dasu irin halin da duniya ta taba shiga. A yayin zantawa da manema labarai, Omveer, mahaifin jaririn ya ce yana jinjinawa gwamnati da yadda take kokarin shawo kan barkewar annobar Coronavirus a kasar, jaridar IndiaToday ta ruwaito. "Ni da mata ta muna jinjinawa matakan da firayim minista Narendra Modi da babban minista Yogi Adityanath suka dauka a kan cutar," yace.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "COVID-19: Lauyoyi sun yi gudun ceton rai bayan wanda ake zargi ya yi tari a kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?