
COVID-19: Gwamnonin Arewa sun amince da haramta Almajiranci a yankin
Wednesday, 22 April 2020
Comment
Kungiyar gwamnonin Arewa ta daga kan cewa ya zama dole a haramta Almajiranci a yankin kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da suke tattaunawa kan matakan da yankin za ta dauka don yaki da annobar coronavirus.
Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ne ya jagoranci taron da gwamnonin 17 suka gudanar ta hanyar amfani da intanet.
A cewar Macham Makut, direktan watsa labarai na Lalong, gwamnonin sun tattauna a kan cibiyoyin gwajin COVID-19 da ke yankin inda suka lura cewa akwai bukatar yin gyare gyare a wasu bangarorin.
Har wa yau, gwamnonin sun amince da kafa a kalla wurin gwaji guda daya a kowane jiha domin saukaka gano masu dauke da cutar da kulawa da su.
Wani sashi na sanarwar ya ce, "A game da batun rufe iyakoki da dokar kulle, gwamnonin sun amince kowace jiha ta cigaba da saka dokokin da ya dace da jihar ta amma sun jadada rufe iyakokin jihohi domin takaita yaduwar cutar.
"Gwamnonin sun kuma tattauna hatsarin da Almajirai ke ciki sakamakon bullar coronavirus inda dukkansu suka amince a haramta almajiranci kuma a mayar da yaran zuwa gidajen iyayensu ko jihohinsu na asali.
"Sun dau alwashin cewa ba za su bari a cigaba da almajirancin ba duba da irin kallubalen da ya ke haifar wa da suka hada da talauci, rashin ilimi, rashin tsaro da rashin tarbiya."
Sanarwar ta kuma ce gwamnonin sun tuntubi Ministan Noma da Cigaban Karkara, Muhammed Sabo Nanono a kan tallafin COVID-19 da za a bai wa manoma a kasar don jin yadda yankinsu za ta amfana da shi.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "COVID-19: Gwamnonin Arewa sun amince da haramta Almajiranci a yankin"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?