
COVID-19: Gawarwaki zasu mamaye titunan kasashen Afirka idan aka yi wasa - Gate
Monday, 13 April 2020
Comment
Uwargidar biloniya Bill Gates ta yi gargadin cewa idan har duniya bata dauki matakin gaggawa da ya dace ba, toh shakka babu za a tsinci gawarwaki a fadin unguwanni a Afrika. Misis Gates ta yi wannan kira ne yayinda ta ke jawabi ga CNN, kan coronavirus da tasirinta a kasashen duniya.
COVID-19: Gawarwaki zasu mamaye titunan kasashen Afirka idan aka yi wasa - Gate Source: Twitter
Ta ce zuciyarta na a Afrika, inda ta bayyana cewa ta damu matuka domin ba lallai ne nahiyar ta iya magance barnar cutar ba.
“Zai munana a kasashe masu tasowa. “Dalilin da yasa har yanzu kuke ganin kamar mutanen da suka kamu a nahiyar basu da yawa, ya kasance saboda basu da wuraren gwaji da yawa. “Duba abunda ke faruwa a Ecuador, suna ajiye gawarwaki a unguwanni,
za ku ga faruwar hakan a kasashen Afrika,” in ji Misis Gates. Melinda Gates wacce ta kasance jigo a gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation ta nuna tsoron cewa abubuwa na iya tabarbarewa a Afrika da zaran lamarin ya girmama, saboda tabarbarewar tsarin lafiyarsu da rashin agaji.
A wani labarin kuma, mun ji cewa wata uwa mai yara biyar da aka ambata da suna, Shabnum Sadiq ta mutu bayan ta kamu da coronavirus a lokacin wani tafiya da ta yi zuwa kasar Pakistan. Matar mai shekara 39 a duniya ta rasu a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, bayan ta yi fama da rashin lafiya sakamakon mummunan cutar, Metro ta ruwaito. Legit.ng ta tattaro cewa matar wacce ta yi aiki a majalisar Slough Borough, Ingila, ta mutu ta bar mijinta da yara biyar, ciki harda 'yan hudu masu shekaru 13.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657 c
0 Response to "COVID-19: Gawarwaki zasu mamaye titunan kasashen Afirka idan aka yi wasa - Gate "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?