--
Covid-19: 'Duk rintsi kar a janye matakan hana tarukan ibada'

Covid-19: 'Duk rintsi kar a janye matakan hana tarukan ibada'


Wata gamayyar kungiyoyin fafutuka da ke rajin inganta bangaren lafiya a Najeriya ta ce har yanzu kokarin kasar na katange kwayar cutar koronabairas a matakin farko yake, don haka bai kamata ta sassauta matakan da ake dauka ba.

A cewarta: "'Yan makwanni masu zuwa na da matukar muhimmanci wajen dakile hauhawar masu fama da annobar a kasar".

Don haka gamayyar ta yi kira ga gwamnonin wasu jihohi su soke shirinsu na janye haramcin da aka sa a kan tarukan addinai da ma sauran taruka har sai hukumar dakile cutuka masu yaduwa da Ma'aikatar lafiya ta tarayya sun ba da shawarar a yi hakan.

"Komai matsin lamba, wannan ba lokaci ne na neman suna a wajen talakawa ba", in ji sanarwar gamayyar HRSC da Mike Egboh da Dakta Chizoba Wonodi suka fitar.

"Shaidu na kimiyya da gogayya da kasashen da suka ci gaba sun mara bayan cewa kauce wa taruka, da yin nesa-nesa da juna da wanke hannuwa da tsaftar jiki har yanzu su ne hanyoyi mafi inganci na riga-kafin yaduwar cutar da mace-macen da ke da alaka da ita."

Ta ce "da yawan mutanen da ke fama da talauci da kuma yawaitar cutuka marasa jin magani kamar hawan jini da ciwon sukari da kuma rarraunan tsarin kula da lafiya, zai zama wani babban bala'i, idan kwayar cutar koronabairas ta fantsama a Najeriya".
Alkaluma daga Hukumar Lafiya ta Duniya da Jami'ar Johns Hopkins sun nuna cewa mutane kimanin miliyan 1 da 600,000 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kuma wasu fiye da 95,000 suka riga mu gidan gaskiya sanadin koronabairas a cikin wata biyar.

Jihohi da dama ne a yankin arewacin Najeriya ciki har da Katsina da Neja suka sanar da dakatar da umarnin hana tarukan Sallar Juma'a da ibadun coci ga mabiya addinin kiristanci.

Sai dai gamayyar ta ce ko da yake, mafi yawan wadanda ke kamuwa da mutuwa sakamakon cutar a kasashen da suka ci gaba suke, amma fa adadin masu kamuwa da mutuwa a Afirka ma yana karuwa.

Mutanen da suka kamu da cutar sun ninka daga daya xuwa 288 a cikin mako shida, baya ga mutum bakwai da suka rasu, haka kuma jihohin da cutar ta bulla cikin sun karu daga daya zuwa 17 ciikin wannan lokaci.

Abin da aka gani a sauran kasashe shi ne matukar ba a dauki tsauraran matakai kamar na kulle garuruwa ba da kuma yin nesa-nesa da juna, adadin masu fama da cutar na iya karuwa ninninkawa cikin dan kankanin lokaci.

HRSC ta ce gwajin da ake yi wa mutane a Najeriya, bai wadatar ba, don haka mai yiwuwa ne ba a iya sanin hakikanin mutanen da ke fama da annobar ba har yanzu.

Gamayyar ta ce abu ne mai matukar yiwuwa cutar ta fara yaduwa a tsakanin al'ummar kasa saboda kashi 85% na mutanen da suka kamu na iya zama wadanda alamomin koronabairas ba su fara bayyana a jikinsu ba, amma duk da suna iya yada kwayar cutar.

Ta bayyana takaici kan yadda aka dage takunkumin da aka sanya a kan gudanar da taruka ciki har da sallar Juma'a da bukukuwan Easter a wasu jihohin kasar duk da ci gaba da samun masu dauke da coronavirus.

"A wasu kasashen alamu na nuna cewa rashin daukar tsauraran matakai kamar hana shige da fice da yin nesa-nesa da jama'a na iya janyo karuwar masu cutar cikin kankanin lokaci," in ji ta.

Ta ce a tsakanin 27 ga watan Fabrairu zuwa 27 ga Maris, adadin masu cutar ya hauhawa a Amurka daga mutum 54 zuwa 100,522, a Italiya kuma daga 593 sai da ya kai 66,414 a cikiin wata guda.

Shawarar da kungiyar ta bayar:

Kungiyar ta HSRC a takaice ta nemi gwamnoni su janye yunkurin da suke ko kuma kokarin soke dage takunkumin da aka sanya kan gudanar da taruka har da na addini har sai hukumar kula da yaduwar cutuka a kasar NCDC da ma'aikatar lafiyar kasar sun ba da shawara a kai.
Kira ga gwamnatin Najeriya da gwamnonin jihohi su kara yawan kayan agaji ga jama'ar da ke da bukata domin saukaka musu ba tare da sun ji bukatar fita domin gudanar da sana'oinsu ba.
Neman 'yan Najeriya su ci gaba da bin shawarwarin masana a bangaren lafiya musamman NCDC da hukumar lafiya ta duniya WHO saboda a cewar kungiyar, babu abin da ya fi muhimmanci fiye da kasancewa a raye.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Covid-19: 'Duk rintsi kar a janye matakan hana tarukan ibada'"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?