--
COVID-19: Buhari zai fara yi wa fursunoni afuwa na musamman a ranar Alhamis

COVID-19: Buhari zai fara yi wa fursunoni afuwa na musamman a ranar Alhamis



 A gobe Alhamis 9 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya za ta fara sakin fursunonin da shugaban kasa ya yi wa afuwa ta musamman a yunkurin ta na rage cinkoso a gidajen na gyaran hali. Leadershi ta gano cewa za a fara sakin fursunonin ne bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bukatar da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya gabatar masa don rake cinkoso a gidajen yarin. Gwamnatin tarayyar ta Najeriya ta dauki wannan matakin ne domin rage yaduwar cutar coronavirus a kasar.

Wannan sakon na cikin wata takardar gayyata ta musamman ne da ofishin ministan ya aike wa manema labarai na gayyatarsu taro a hedkwatan hukumar kula da gidajen gyaran hali na kasa (NCoS. Mai magana da yawun hukumar da NCoS, DCC A.C. Njoku ne ya saka hannu a kan sakon.

Ministan zai jagorancin wata tawaga ta musamman zuwa gida gyaran hali na Kuje da ke Abuja domin kaddamar da shirin.KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: Buhari zai fara yi wa fursunoni afuwa na musamman a ranar Alhamis "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?