--
Covid-19: Buhari zai bayyana tsauraran matakai mako mai zuwa - NCDC

Covid-19: Buhari zai bayyana tsauraran matakai mako mai zuwa - NCDC

- Darakta janar din Hukumar Yaki da Cututtuka masu Yaduwa ta kasa, ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bayyana tsauraran hukunci a kan annobar - Dr Chikwe Ihekweazu ya ce a gobe Laraba ne Shugaban kasar zai yi tattaunawar hadaka da gwamnoni don sanar da hukunci a kan covid-19

- Gwamna Masari ya roki shugaban kasa da a samar da dakin gwajin kwayar cutar a jihar don ana samun tsaiko kafin a samu sakamakon samfuri idan an diba Darakta janar din hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa, Dr Chikwe Ihekweazu ya sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu zai bayyana wasu tsauraran hukunci a kan yakar annobar Coronavirus a mako mai zuwa.

Ya ce: "A ranar Laraba mai zuwa ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wayar tarhon hadaja da gwamnoni kuma zai sanar da wasu tsauraran matakan a kan tattalin arziki."

Shugaban NCDC din ya sanar da hakan ne a yayin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari a gidan gwamnatin jihar da ke Katsina. Ya yi jawabi ne a yayin da gwamnan ya bukaci kafa wurin gwajin cutar a Katsina don gaggauta samun sakamakon wadanda ake zargin suna dauke da cutar a jihar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, Masari ya ce ana tafiyar sa'o'i 12 daga jihar kafin a samu wurin gwajin kwayar cutar a Abuja. Ya ce: "Samar da dakin gwajin cutar a jihar zai taimaka wajen rage tsawon lokacin samun sakamako da kuma wahalar da muke sha a yayin kaiwa. "Samfurin jini idan an diba a Katsina suna daukar a kalla sa'o'i 24 kafin su isa Abuja a samu gwadasu."

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Related Posts

0 Response to "Covid-19: Buhari zai bayyana tsauraran matakai mako mai zuwa - NCDC "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?