
Covi-19: Muna bukatar tallafin coronavirus-Gwamnan Kano
Tuesday, 21 April 2020
Comment
Gwamnan Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bai wa jiharsa tallafin kudade domin yaki da coronavirus a daidai lokacin da masu kamuwa da cutar ke karuwa a jihar.
Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Litinin a yayin wata ziyara da Darekta Janar na Hukumar Yaki da Yaduwar Cutuka ta Najeriya, NCDC, Dr. Chikwe Ihekweazu ya kai masa domin ganin irin kintsawar da Kano ta yi wajen tunkarar wannan annoba.
Ganduje ya ce, sun samu sama da miliyan 500 da wasu kayayyaki da za a fara raba su nan kusa ga al’umma, yana mai cewa, sun kafa kwamitocin da za su tabbatar cewa, talakawa sun samu tallafin rage radadin da coronavirus ta jefa su a ciki.
Sai dai duk da wannan hubbasawar ta gwamnatin, kawo yanzu babu wani tallafi daga gwamnatin tarayya duk da cewa, Kano ce ta uku a jerin jihohin da suka fi fama da wannan annoba a Najeriya a cewar gwamnan.
Tuni gwamnatin tarayya ta bai wa jihar Lagos tallafin Naira biliyan 10 don yaki da cutar ta COVID-19.
Amma Ganduje ya ce, Kano ta fi jihar Lagos bukatar agaji , lura da cewa, Lagos ta fi Kano karfin tattalin arziki.
Darekta Janar na hukumar ta NCDC, ya yi alkawarin cewa, za su samar da wani tsarin tallafa wa Kano don ganin cewa, ta shawo kan kalubalen da ke gabatanta dangane da cutar coronavirus.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Covi-19: Muna bukatar tallafin coronavirus-Gwamnan Kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?