
Covi-19: Ansamar Da Cibiyar gwajin coronavirus a jihar kano
Friday, 10 April 2020
Comment
Kafa wannan cibiyar cika alkawari ne da gwamnatin tarayya tayi na samar da dakin bincike na musamman domin gwajin cutar COVID-19 a Kano da wasu jihohin Arewa maso yamma.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, wanda ya kai ziyarar ganin ido cibiyar a daren Alhamis ya bayyana cewa daga yanzu za a fara gwaji a Kano.
Yace: “Daga yanzu, ba za a sake kai samfurin jinin mutane Abuja ba domin gwaji. A Kano za a yi.“
“Mun zo yawon ganin ido domin tabbatar da abinda ke kasa ne, kuma bisa abinda muka gani a cikin dakin gwajin, an kammala shirya kayayyakin kuma an fara gwaji.“
Ya mika godiyar gwamnatin jihar Kano karkashin gwaman Abdullahi Umar Ganduje, ga gwamnatin tarayya bisa wannan cibiya a Kano.
Yayinda suke zagaye cikin cibiya, wani maaikacin NCDC, AbdulMaid Musa, ya ce babu irin gwain da ba za a iya ba a cibiyar.
Hakazalika an fara horar da maaikatan asibitin AKTH da gwamnatin jihar kan yadda zasu rika amfani da kayayyakin.
Shugaban asibitin AKTH, Farfesa Abdurrahaman Sheshe, ya yabawa jajircewan kwamitin yakar Coronavirus ta jihar karkashin jagorancin mataimakin gwamnan bisa yaddaaka wayar da kan mutane kan matakan takaita yaduwar cutar.
Gabanin kafa wannan cibiya, babu wajen gwajin cutar Coronavirus ko daya a jihohin Arewacn Najeriya 19.
Birnin tarayya Abuja ake kai samfurin mutanen Arewa sannan a dawo da sakamakon.
Kano ta shiga sawun jihohi irinsu Legas, Edo, Osun, Oyo, da Abuja masu cibiyar gwajin cutar.KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Covi-19: Ansamar Da Cibiyar gwajin coronavirus a jihar kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?