--
Coronavirus: An yanke wa dan sanda hannu a Indiya

Coronavirus: An yanke wa dan sanda hannu a Indiya

An yanke hannun wani dan sanda yayin da yake kokarin tabbatar da dokar hana fita a Jihar Punjab da ke arewacin Indiya.

Kazalika an raunata wasu abokan aikinsa biyu a harin.

Lamarin ya faru ne a unguwar Patiala a lokacin da wata mota ta afka kan wani wurin binciken ababen hawa. Matuka motar ne kuma suka fito suka fara kai wa 'yan sandan hari.

An kama akalla uku daga cikin maharan da aka ce 'yan wata kungiyar addini ne.

Shugaban 'yan sandan Punjab ya fada wa NDTV cewa bayan artabu na tsawon sa'a biyu miyagun sun "mika wuya dauke da wukake da takubba".

An sha kai wa 'yan sanda hari a wasu sassan kasar a yunkurinsu na tilasta wa mutane bin dokar hana zirga-zirga da aka saka domin dakile yaduwar annobar cutar Covid-19.


KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Coronavirus: An yanke wa dan sanda hannu a Indiya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?