--
Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar

Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar


- Cutar coronavirus ta halaka wata uwa mai yara biyar da aka ambata da suna Shabnum Sadiq - An tattaro cewa matar mai shekaru 39 ta kwashi cutar ne a yayin wani tafiya da ta yi zuwa Pakistan - Marigayiyar, wacce ta kasance mai ba da shawara a Slough, Ingila, ta bar yara biyar ciki harda 'yan hudu Wata uwa mai yara biyar da aka ambata da suna,
Shabnum Sadiq ta mutu bayan ta kamu da coronavirus a lokacin wani tafiya da ta yi zuwa kasar Pakistan. Matar mai shekara 39 a duniya ta rasu a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, bayan ta yi fama da rashin lafiya sakamakon mummunan cutar, Metro ta ruwaito. Legit.ng ta tattaro cewa matar wacce ta yi aiki a majalisar Slough Borough, Ingila, ta mutu ta bar mijinta da yara biyar, ciki harda 'yan hudu masu shekaru 13.

Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar Source: UGC 
Jigon majalisa James Swindlehurst ya ce: “Hakan ya taba zuciyarmu gaba daya sannan tunaninmu na tare da iyalai da abokanta. “Shabnum ta kasance mai bada shawara da ta jajirce kan aiki, kuma duk da cewar wannan ne zangonta na farko, ta bayar da gudunmawa fiye da shekarun da ta yi a zauren majalisar. “Mun yi aiki tare kai da fata kuma, nayi kewanta sosai. Wannan gagarumin rashi ne ga majalisar da garin, amma hakan bai kai rashin da iyalanta da makusanta suka yi ba."

A wani rahoton kuma, mun ji cewa gwamnatin jahar Lagas a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, ta tabbatar da mutuwar wani mara lafiya sakamakon cutar coronavirus a jahar. Kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi, wanda ya bayyana hakan a shafin Twitter, ya ce a yanzu mutane biyar kenan suka mutu a jahar. Ya ce mutumin ya rasu ne sakamakon tabarbarewar lafiya da ke da nasaba da coronavirus. Abayomi ya kara da cewa an samu sabbin mutane 11 da suka kamu a ranar Asabar. A yanzu jahar na da jimlar mutane 177 da suka kamu da COVID-19.


KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657 c

Related Posts

0 Response to "Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?