--
Coronavirus ta kusan kama 'yan Afrika miliyan 10-WHO

Coronavirus ta kusan kama 'yan Afrika miliyan 10-WHO



Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi hasashen cewa, za a iya samun karuwar mutane milyan 10 sabbin kamuwa da cutar coronavirus a nahiyar Afrika nan da watanni 3 zuwa 6 masu zuwa duk da kasasncewar nahiyar  mafi karancin masu dauke da cutar a yanzu.

Hasashen WHO na zuwa ne duk da matakan da gwamnatocin kasashen nahiyar ke dauka na killace jama'a a gida don dakile yaduwar cutar.

Sai dai Michael Yao, shugaban Sashen Agajin Gaggawa na WHO, reshen Afrika ya ce, ba lallai hasashen hukumar ya iya zama gaskiya ba, kamar dai hasashen da ta yi lokacin annobar Ebola na yiwuwar mutuwar miliyoyin jama'a amma kuma hakan bai tabbata ba, saboda matakan kariyar da jama'a suka dauka.

Acewar Michael Yao, matakan lafiyar da ake dauka da ma damarar da jama'a suka daura na hana yaduwar cutar matukar suka ci gaba da tabbata ko shakka babu, hasashen hukumar ba zai tabbata ba.

Kawo yanzu dai fiye da mutum dubu 17 aka tabbatar sun kamu da cutar ta corona a nahiyar Afrika ciki har da 900 da suka mutu, adadin da ke nuna nahiyar a matsayin mafi karancin masu dauke da cutar.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/




LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Coronavirus ta kusan kama 'yan Afrika miliyan 10-WHO"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?