--
Coronavirus: Mutum na farko ya mutu, 21 sun kamu a Kano

Coronavirus: Mutum na farko ya mutu, 21 sun kamu a Kano



A karon farko an samu mutum na farko daya mutu sakamakon cutar coronavirus a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Adadin mutanen da suka kamu da cutar kawo yanzu ya kai 21 a jihar, bayan an sanar da karin mutum 12 da suka harbu da cutar a daren Laraba.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma'aikatar lafiya ta jihar kano ta ce ya zuwa karfe 11:45 na daren Laraba, "adadin masu dauke da cutar a Kano ya kai 21."

Da misalin 11:55 ta kuma sake wallafa wani sakon da ke tabbatar da mutuwar mutum na farko sakamakon cutar.

Wannan adadi na zuwa ne kasa da kwanaki biyar da aka samu bular cutar karo na farko a Jihar.


A ranar Asabar ne hukumomi suka sanar da manema labarai cewar wani mutum ya kasance na farko wanda ya kamu da cutar a jihar.

Bayanan da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutumin, wanda yake zaune a karamar hukumar Tarauni, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajibirin ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.

Gwamnatin jihar ta Kano ta yi feshin magani a wurare biyar da mutumin ya kai ziyara kafin a gano yana dauke da cutar.

 A hirarsa da BBC kan bullar cutar coronavirus a Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce za a dauki tsauraran matakai domin kare al'ummar jihar.

Daga cikin matakan, Gwamnan ya haramta wa 'A daidaita sahu daukar mutum fiye da daya', ko da yake daga bisani an amince a rka daukar mutum biyu.

Su ma motocin haya, an hana su daukar mutane fiye da kima.

Kazalika, gwamnatin jihar ta ce za ta dauki matakai na rufe wasu kasuwanni tana mai cewa za a bar kasuwannin da ke sayar da kayan abinci da sauran kayan bukatar gaggawa su ci gaba da budewa.

Da ma tuni aka samu bullar cutar a jihohin da ke makwabtaka da Kano, wato Kaduna da Katsina.

Hukumar da ke dakile cututtuka masu yaduwa NCDC ta ce ya zuwa Talata da maraice ta tabbatar da cewa mutum 373 ne suka kamu da cutar, 99 suka warke yayin da 11 suka mutu a fadin kasar.
KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Coronavirus: Mutum na farko ya mutu, 21 sun kamu a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?