--
Coronavirus: 'Matsala ce ta siyasa, ba ta lafiya ba' - Yuval Noah Harari

Coronavirus: 'Matsala ce ta siyasa, ba ta lafiya ba' - Yuval Noah Harari


Zabin da muka yi na yaki da cutar Covid-19 zai sauya duniya nan da shekaru masu zuwa, In ji wani masanin tarihi dan kasar Isra'ila Yuval Noah Harari, marubucin littafin Sapiens: da yayi magana kan takaitaccen tarihin dan adam.
Wacce irin al'umma za mu zama lokacin wannan annoba? kamata ya yi kasashe su zama tsintsiya madaurinki daya? ko kuma kowa ya yi ta kansa? tsare mutane da sanya ido kansu ne matakan da ya kamata a dauka kan 'yan kasa ko kuma kama-karya?

"Wannan rikicin ya sanya mu daukan tsauraran matakai kuma cikin gaggawa. amma duk da haka muna da zabi" Harari. Ya shaida wa shirin BBC Newshour.
Rikicin "siyasa"

"Watakila zabi biyun da muke da su sune, ko dai mu tunkari wannan matsala ta hanyar ko wacce kasa ta ware kanta ko kuma hada gwiwa kan yakar abin da ya addabi duniya baki daya tare da nuna kishin juna,"

"Na biyu a mataki na ko wacce kasa, muyi kokari muga bayanta ta hanyar kama-karya ga yan kasa komai ya koma hannun gwamnati ta kuma rika sanya idanu, ko kuma ta hanyar sadaukarwa tare da karfafa al'amuran yankasa.

Annobar coronavirus ta janyo tambayoyi biyu, tambaya ta bangaren kimiyya da kuma siyasa, in ji Harari.
Amma yayin da muke warware kalubalen ta fuskar kimiyya, muna kuma daukar darasin yadda zamu tunkare ta ta fuskar siyasa.

"Duniya tana da duk abin da take bukata don cin galaba kan wannan annoba," kamar yadda yace.

"Yanzu ilimi ya wadata ba kamar lokacin annobar Black Death ba ne (wadda ta kashe kashi daya cikin uku da adadin mutanen nahiyar Turai) ba wai mutane na mutuwa bane ba tare da sanin dalili ba, ba kuma musan mai za mu yi a kai bane."

Tuni China ta bankado cewa cutar Sars-CoV-2 ita take haddasa wannan annoba, kuma kasashe da dama sun yi irin wannan bincike.
 captionLikitoci a Italiya na aiki kan gano musabbabin wannan cuta, yayin da kasar ke ci gaba da kasance wa a kulle a wani mataki na dakile yaduwar cutar.

Kazalika Covid-19 bata da magani, masu bincike na ta fadi tashi wajen binciken rigakafin cutar ta hanyar fasahar zamani mafi inganci a fannin kiwon lafiya.

Mun kuma san rawar da matakan wanke hannu da ba da tazara ke takawa wajen kare mu daga cutar da kuma yadda suke hana yaduwarta.
"Muna sane da hadarin da ke fuskantarmu muna kuma da fasahar zamani, muna da karfin tattalin arziki da za mu iya cin nasara a kanta," in ji Harari.

"Tambayar kawai shi ne ta ya ya za mu yi amfani da wannan damar ta mu? wannan kuma tambaya ce da ke da alaka da siyasaKARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Coronavirus: 'Matsala ce ta siyasa, ba ta lafiya ba' - Yuval Noah Harari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?