
Coronavirus: Ku zauna a gida ku wanke hannuwa - Buhari
Sunday, 12 April 2020
Comment
Mai magana da yawun shugaban Najeriyar, Garba Shehu ya ce Buhari ya kuma godewa al'umma bisa hakuri da suka yi, da kuma kwarin gwiwar da suke bayarwa wajen yaki da barkewar cutar covid-19.
Ya ambato shugaban na cewa "Mun fahimci a yau, za a samu 'ya'ya maza da mata wadanda ba za su iya ziyartar iyayensu ba, da kuma dattawan da aka kebe daga matasa. Akwai kuma wadanda ke rayuwa hannu baka hannu kwarya kuma suna fuskantar wahala,"
"Dole ne mu sake kira kan ci gaba da mutunta umarnin takaita zirga-zirga a jihohin da wannan umarni ke aiki tare da bin shawarwarin likitoci da masana kimiyya: zama a gida da wanke hannaye da kuma kare rayukan jama'a,"
A cewarsa "'yancin walwalarku da muke neman a yau ku takaita zai zama na wani dogon lokaci ne kawai idan masu ba da shawara kan kimiyya suka ce hakan ya zama dole. Amma suna da mahimmanci - a fadin duniya - a kawo karshe tare da yaki da yaduwar cutar,"
Shugaban ya kara da cewa gwamnati ta yi wa dunbim marasa karfi da ke yankunan da matakin kullen ya shafa tanadin tan 70,000 na hatsi wanda za a rarraba ga wadanda suke da tsananin bukata da kuma rarraba kudaden tallafi da gwamnatin tarayya ke yi a jihohin da kananan hukumomi.
"Muna rokonku ku saurari sanarwar da ake a kafafen yada labarai kan hanyoyin samun tallafin gwamnatin da kuma sanin irin tallafin da gwamnati ta tsara yi a nana gaba,".
"Juriyar da gwamnati take so daga gareku saboda a fadin duniya babu wata hanya daya tilo ta yaki da annobar. Babu rigakafi kuma hakan na nufin akwai zabi da za a yi: tsakanin ci gaba da tafiyar da lamura kamar yadda aka saba ko rungumar takunkuman da aka sanya na takaita zirga-zirga duk da hana ya yi mummunan tasiri da ba a yi tsammani ba." a cewar sanarwar.
"Amma a wannan lokaci na rashin dadi, ya zama dole a garemu mu fada muku gaskiya ba tare da boye-boye ba: wannan annoba ce ta duniya baki daya. Ta shafi kasashe 210 da yankuna a sassan duniya. Ba zamu nade hannu muna jiran taimakon wasu ba. Mune kadai za mu iya yakar cutar,"
"A maimakon haka, kawar da kwayar cutar ya ta'allaka a kanmu. Ba zamu jira wasu ba. Za mu iya dogara ne da kanmu. Kuma hakan ya zama dole a yi kuma za mu yi nasara ta kawo karshen barkewar cutar a matsayinmu na 'yan Najeriya tare."
Ya zuwa yanzu dai mutum 318 ne suka kamu da coronavirus a kasar - mutum 70 sun warke sai wasu 10 da suka mutu.
KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Coronavirus: Ku zauna a gida ku wanke hannuwa - Buhari"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?