--
Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano

Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano



 Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara cibiyar killace masu dauke da cutar covid-19 da gidauniyar Dangote tare da hadin gwuiwar gwamnatin jihar Kano suka samar. Cibiyar, mai jimillar gadon kwantar da marasa lafiya 509, tana da bandakuna, dakin gwaji, dakin shan magani, motar daukan marasa lafiiya,


dakin ganawar ma'aikata da masana da sauransu. Tun a ranar 29 ga watan Maris Legit.ng ta wallafa rahoton cewa hamshakin attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, zai samar da wata cibiyar killace wa mai gado 600 domin duba wadanda suka kamu da kwayar cutar coronvirus a jihar Kano. Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da kwamitin neman kudin taimakawa masu karamin karfi a jihar.


H.E @GovUmarGanduje inspected the Kano State Isolation Centre at Sani Abacha Stadium which is being setup by Dangote Foundation in Collaboration with the State Govt. The centre will have a total of 509 beds, toilets, lab, chemist, ambulance, briefing room, and other facilities. pic.twitter.com/iKYM1yMhnA
 Hakan na kunshe ne a cikin wani gajeren sako da Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa a bangaren sabbin kafafen sadarwa, ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta a ranar Lahadi, 28 ga watan Maris.


A baya an ji tsoron cewa mai gidauniyar Dangote kuma hamshakin attajirin dan kasuwa, Alahji Ali Dangote, zai iya kamuwa da kwayar cutar coronavirus bayan ya yi mu'amala da Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da aka tabbatar da cewa yana dauke da kwayar cutar.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Dangote ya bayyana cewa ya yi gwajin kwayar cutar covid-19 ne a matsayinsa na dan kasashe da dama sannan shugaba a kasuwanci. Ya ce yana jagorantar shugabannin a bangaren kasuwanci domin taimakon gwamnati a kokarinta na dakile yaduwar cutar.


KARANTA: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

DAGA MUJALLAR:https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?