--
Coronavirus: An hana cin mage da kare a Shenzhen na China

Coronavirus: An hana cin mage da kare a Shenzhen na China

Shenzhen ya kasance birni na farko a China da ya haramta sayarwa da cin naman kare da mage.

Wannan na zuwa ne bayan alakanta cutar coronavirus da cin namun daji, dalilin da sa ya hukumomin China suka haramta ci da sayar da naman dabbobin.

Dokar haramta cin mage da kare za ta fara aiki ranar 1 ga watan Mayu a Shenzhen.

Wata kungiyar kare hakkin dabbobi ta (HSI) ta ce karnuka miliyan 30 ne ake kashewa a sassan Asia domin nama.

Sai dai ba a fiye cin naman kare a China ba- yawancin 'yan China sun ce ba su taba ci ba kuma ba za su ci ba.

"Kare da mage sun fi shakuwa da mutane fiye da sauran dabbobi, kuma haramta cin naman kare da mage ba sabon abu bane a kasashen da suka ci gaba har da Hong Kong da Taiwan," kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuter ya ruwaito gwamnatin birnin Shenzhen na cewa.

Kungiyar HSI ta yaba wa Shenzhen da daukar matakin.

"Wannan yunkuri ne da zai kawo karshen mummunan kasuwancin da ke kisan kusan karnuna miliyan 10 da mage miliyan 4 a China duk shekara," in ji Dr Peter Li, jami'in HSI.

Kasuwar naman dabbobin daji
A watan Fabrairu ne hukumomin China suka haramta cin naman dabbobin dawa.

Matakin na zuwa ne bayan ta bayyana cewa kasuwar Wuhan da ake sayar da namun dajin nan ne tushen barkewar cutar coronavirus, inda ake tunanin daga dabbobin aka samu cutar.

Yadda ake ta yada labarai game da cin naman dabbobin ne ya sa gwamnatin China ta fara daukar matakai kan kasuwannin da ake sayar da naman dabbobin dajin.
LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Coronavirus: An hana cin mage da kare a Shenzhen na China"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?