--
Coronavirus: Gwamnatin Kano ta bude shafin yanar gizo na daukan ma'aikatan lafiya

Coronavirus: Gwamnatin Kano ta bude shafin yanar gizo na daukan ma'aikatan lafiya



Gwamnatin jihar Kano ta bude shafin yanar gizo domin fara rijistar masu shawa'ar zama 'yan agaji a bangaren kiwon lafiya domin taimakawa jihar a yakin da take yi da yaduwar annobar cutar covid-19. Jami'ar hulda da jama'a a ma'aikatat lafiya ta jihar Kano, Hadiza Namadi, ce ta fadi hakan ranar Alhamis a cikin wani sako da ta aikwa manema labarai.

Hadiza ta bayyana cewa gwamnati ta gayyaci wadanda suka nemi aikin domin tantancewa, wacce aka fara ranar Laraba, amma aka dakatar saboda yawan masu neman aikin da suka cushe wurin tantancewar.. "A kokarin gwamnati na shawo kan cunkuson masu sha'awar aikin, shine a bude shafin yanar gizo domin takaita wa masu sha'awar aikin wahala," a cewar saanarwar.

Coronavirus: Gwamnatin Kano ta bude shafin yanar gizo na daukan ma'aikatan lafiya Source: Facebook 

Ma'aikatan lafiyar 'na sa ka' da ake nema sun hada likitoci, ma'aikatan kula da lafiyar al'umma, masu karatun taimakon likitoci a asibiti da sauran kwararru a bangaren aikin lafiya.

Sauran ragowar ma'aikatan lafiyar da ake nemaa sun hada da masu kimiyyar gwaje-gwaje a asibiti, masana kimiyyar magunguna, malaman tsafta da sauransu.. Ana bukatare masu sha'awar agajin su kasance mazauna Kano. Shafin neman aikin shine kamar haka: www.kanostate.gov.ng/volunteers. Jihar Kano na daga cikin jihohin sa suka kasance a sahun gaba wajen saka dokar rufe iyakoki, kasuwanni da hana walwalar jama'a saboda barazanar annobar covid-19


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Coronavirus: Gwamnatin Kano ta bude shafin yanar gizo na daukan ma'aikatan lafiya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?