--
Coronavirus: Gwamnan Riyadh, yan gidan sarautar Saudiyya 150 sun kamu da cutar

Coronavirus: Gwamnan Riyadh, yan gidan sarautar Saudiyya 150 sun kamu da cutar

Yan gidan sarautar kasar Saudiyya akalla 150 sunkamu da cutar Coronavirus a makonni baya-bayan nan, rahotanni sun bayyana. A cewar New York Times, gwamnan Riyadh, babbar birnin kasar Saudiyya, Yarima Faisal bin Bandar bin Abdulaziz Al Saud,

mai shekaru 70 na kwance a asibiti bayan kamuwa da cutar. Tuni Sarkin Saudiyya, Salman bin AbdulAziz, da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, sun killace kansu gudun kada su harbu da cutar. Likitocin asibitin tunawa da Sarki Faisal dake kula da yan gidan sarauta ta shirya gadaje 500 don kula da su.

Gwamnan Riyadh, yan gidan sarautar Saudiyya 150 sun kamu da cutar Source: UGC 

Asibitin ta fitar da sakon kar ta kwana ga manyan Likitocin asibitin cewa a shirya domin za a kawo wasu marasa lafiya masu uwa a gindin murhu. Jawabin yace "Bamu san adadin mutanen da za a kawo ba amma mu kasance a shirye. A fitar da dukkan sauran marasa lafiya masu cutuka mai tsanani."

Sakon ya kara da cewa daga yanzu za a rika jinyar ma-aikatan asibitin a wani asibiti daban saboda a samu isasshen gadaje ga yan gidan sarauta. Akwai dubunnan yarimomi a gidan sarauta kuma sukan yi tafiye-tafiye da dama kasashen Turai. Ana kyautata zaton daga kasashen Turai suka kwaso cutar zuwa Saudiyya Kasar Saudiyya mai adadin mutane milyan 33 ta tabbatar da mutane 2,932 sun kamu da cutar kuma 41 sun rmutu. Ministan kiwon lafiyar kasar,

Tawfiq al-Rabiah, a ranar Talata ya yi gargadin cewa da alamun kasar zata fuskanci babban kalubale cikin makonni masu zuwa. Tawfiq al-Rabiah yace "Cikin makonni masu zuwa, bincike ya nuna cewa kimanin mutane 10,000 zuwa 200,000 zsu kamu da cutar (a saudiyya)."

Idan baku manta ba, hukumomin Masallatai biyu masu daraja sun dakatad da Sallolin Jumaa a Makkah da Madinah sai lokacin da Allah yayi saboda gudun yaduwar cutar. Hakazalika an dakatad da ibadar Umrah kuma da yiwuwan ba za a yi Hajjin bana ba. Kasar ta umurci dukkan hukumomin jin dadin alhazan kasashen duniya su jinkirta amsan kudi hannun alummarsu tukun.


KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Coronavirus: Gwamnan Riyadh, yan gidan sarautar Saudiyya 150 sun kamu da cutar "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?