--
Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Don samun nasara a yaki da annobar coronavirus, dole ne 'yan Najeriya su ajiye addini tare da rungumar ilimi, inji shugaban One Love Family, Sat Guru Maharaj Ji. A yayin zantawa da manema labarai a garin Legas, Maharaj Ji ya ce hanya daya kuma mafita ga 'yan Najeriya ita ce amfani da sunan Ubangiji kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce, "Mun gano cewa kalmar Ubangiji bata da ma'ana kuma ana amfani da ita ne hana mutane morar albarka daga Ubangiji. Dole ne jama'a su bar addinai kwata-kwata sannan a samu mafita." Ya kara da cewa, "Idan mutum ba bukatar aiki, babu amfanin kabila ko addini. Abu ne da ba za a iya hanawa ba, za a iya kafa shi. Coronavirus matacciya ce a duk lokacin da muka hada kai tare da rungumar juna."

Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji Source: Twitter Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, Maharaj Ji ya ce, "kowa ya san cewa addinai ba za su iya maganin coronavirus ba. An rufe Saudi Arabia, Makka, Madina da kuma hanyoyi. A yanzu ina karfin Musa na raba ruwa biyu? Ina karfin Dawud? Babu abinda ya gagari Ubangiji. Rayuka na ta salwanta saboda rashin ilimi." A ranar 6 ga watan Afirilu, masu cutar Coronavirus a Najeriya sun kai 238, an sallami mutane 35 daga asibiti inda mutane biyar suka rasa rayukansu.

A watan da ya gabata, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da cutar coronavirus. An kuwa kai shi cibiyar killace mutane masu cutuka masu yaduwa ta Abuja inda daga bisani aka mayar dashi Legas. A yayin zantawa da manema labarai, Maharaj Ji ya zargi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar da yaudara.

A don haka yayi kira da a hukunta shi. "Ka je kasar waje har zuwa kasar China kuma kana sane da cewa akwai matsaloli. Ya kamata a ce ya killace kansa na kwanaki 14 amma ya ki yin hakan. Waye shi kuma meye burinsa?" Ya kwatanta hana walwala da aka yi sassan kasar nan da lamari mai tsoratarwa.

Ya kara da kira ga gwamnatin da ta samar da hanyoyin gwajin cutar a sassan fadin kasar nan. "Ba mu san me ke faruwa a kasar China da Turai ba. Bamu san me suke cewa ba. Mu nemi hanyar yakar cutar nan. Ba za mu hada kanmu da wasu ba. Suna cin abinci ba irin namu ba. Kamar yadda muka yaki cutar Ebola, ba mu bi yadda suka suka bi ba."


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?