--
Coronavirus: Ana zanga-zangar rashin amincewa da dokar hana zirga-zirga a Amurka

Coronavirus: Ana zanga-zangar rashin amincewa da dokar hana zirga-zirga a Amurka

An gudanar da zanga-zanga a jihohin Arizona da Colorado da Montana da Washington ranar Lahadi, biyo bayan wasu da aka gudanar a jihohi shida na kasar.

Sun bukaci a saukaka dokar takaita zirga-zirga, duk da hadarin kamuwa da cutar korornar idan aka sake bude tituna da makarantu da ofisoshi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna goyon bayansa ga zanga-zangar.

Amurka ta zamo cibiyar annobar, inda kusan mutum 735,000 suka kamu kuma 400,000 suka mutu - amma alamu sun fito da ke nuna cewa kasar ta kai kololuwar annobar kuma a wasu jihohin ma an fara samun ragi a masu kamuwa da cutar.

A jihar Washington, daya daga cikin jihohin da cutar ta shiga ta yi barna, daruruwan mutane sun taru a babban birninta, Olympia, suna bukatar gwamna ya sassauta dokokin da suka takaita gudanar da kasuwanci.

'Yan sanda sun yi kiyasin cewa mutane 2,500 ne suka halarci zanga-zangar, kuma ta kasance daya daga cikin zanga-zanga mafi girma da aka yi don nuna adawa da dokar hana fita da zirga-zirga a Amurka a makon da ya wuce, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Da yawa daga masu-zanga-zangar sun yi watsi da dokar nan ta barin tazara, da magiyar da wadanda suka shirya tattakin suka yi masu, kan su sanya takunkumin rufe hanci.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito cewa, a jihar Montana daruruwan masu zanga-zangar sun yi nasu tattakin a Helena.

A birnin Denver na jihar Colorado ma, an yi tattakin mai kwatankwacin na Montana, inda masu zanga-zangar suka yi tururuwa a majalisar dokokin jihar don nuna adawa da dokar barin tazara.

Yayin da masu zanga-zangar suka cika tituna da motoci, a daya bangaren ma'aikatan lafiya ne sanye da kayan aikinsu da takunkumin rufe hanci da baki suka tsaitsaya don nuna adawa da masu zanga-zangar.

Gwamman motoci sun ta kewaye ginin majalisar yayin da kusan mutum 200 suka jejjeru a farfajiyar gaba ginin suna dauke da kwalaye da tutoci.

A jihar Arizona, masu zanga-zanga sun shiga motoci - an yi kiyasin kusan guda 100 - suka rika kewaye ginin majalisar dokokin jihar a Phoenix don janyo cunkoson motoci, a cewar wasu rahotanni.

Gwamnoni a jihohi da dama sun fara tattauna yadda za su bude jijohinsu duk da alamomin durkushewar tattalin arziki, amma wasu yankunan na ci gaba da zama cikin tsauraran dokokin hana zirga-zirga.

Gwamnan jihar California, Gavin Newsom shi ne na farko a kasar da ya fara sanya dokar zama a gida a jihar mafi yawan mutane a kasar tun ran 19 ga watan Maris.

Makwatanta jihohin Washington da Oregon sun bi sahu bayan 'yan kwanaki. Wannan ya jefa mazauna wadannan jihohi 11.5, idan aka hada su, karkashin dokar zama a gida tun 23 ga watan Maris

A wannan mako ne gwamnan New York Andrew Cuomo, ya sanar da cewa jiharsa za ta tsawaita dokar hana fitanta zuwa 15 ga watan Mayu.

A lokacin da yake Magana ranar Lahadi, a taronsa na kullum da yake yi da manema labarai kan annobar, Mista Cuomo ya gargadi mazauna jihar da su daure su ci gaba da zama a gida.

"Dole ne mu tabbatar da cewa mun dakile cutar nan," in ji Mista Cuomo. "Dole mun kosa mu ci gaba da rayuwa yadda muka saba."

Mista Trump, dan jam'iyyar Republican, ya nuna alamun ya goyi bayan zanga-zangar ta nuna adawa da dokokin dakatar da ayyuka cik, wadanda kuma ake bukata don hana yaduwar cutar.

Ranar Juma'a y ace dokokin da aka sa a Minnesota da Michigan da Virginia sun yi "tsauri da yawa".

Gwamnan jihar Washington, Jay Inslee ya ce goyon bayan da Shugaban kasar ke nuna wa masu zanga-zangar na da "hadari", kuma ya yi dai-dai da bijirewa dokokin jihohin.

"A ce an samu Shugaban Amurka yana karfafa wa mutanen da ke saba doka gwiwa, ba zan iya tuna lokacin da muka taba samun iorin haka ba a Amurka tunda nake raye," ya shaida wa tashar ABC ranar Lahadi.

Nancy Pelosi, kakakin majalisar wakilai ta jam'iyyar Democrat ta zargi Mista Trump da goyon bayan zanga-zangar don ya dauke hankalin jama'a.

"Goyon bayan shugaban ga wannan zanga-zanga, dauke hankalin mutane ne daga batun cewa bai dauki matakan da suka dace ba wajen yin gwaji da bayar da kulawa da binciko wadanda ake tunanin sun kamu da kuma killace masu dauke da cutar," ta shaida wa ABC.

Ranar Asabar ne masu zanga-zangar suka cika titunan Annapolis a Maryland, suna busa ham din mota don nuna rashin amincewarsu da matakan hana zirag-zirgar.

Sama da mutum 200 ne suka yi tattaki a kofar gidan gwamnan jihar Indiana, yayin da kusan mutum 200 suka taru a Austin, babban birnin jihar Texas. Jihar New York ma ta fuskanci zanga-zangar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Related Posts

0 Response to "Coronavirus: Ana zanga-zangar rashin amincewa da dokar hana zirga-zirga a Amurka"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?