--
Buhari ya ce babu shiga babu fita a Legas da Abuja, amma zasu cigaba da raba kudade

Buhari ya ce babu shiga babu fita a Legas da Abuja, amma zasu cigaba da raba kudade



Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnati za ta cigaba da rabon kudi da kayan abinci ga gajiyayyu da talakawa yayin da ya kara wa’adin dokar ta-baci a Abuja da jahohi biyu. Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi ga yan Najeriya a daren Litinin, inda yace duba da shawarwarin da ya samu, ya tsawaita wa’adin dokar ta baci da mako 2.

Buhari yace tsawaita dokar ya zama dole domin kare yaduwar cutar a Najeriya, duba da cewa jahar Legas da babban birnin tarayya Abuja ne suka fi yawan masu dauke da cutar. Kididdigan hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC ya nuna akwai fiye da mutane 300 dake dauke da cutar a Najeriya, yawancinsu kuma sun fito ne daga Abuja da Legas.

Saboda tsawaita dokar, Buhari ya ce gwamnati ma za ta tsawaita rabon kudade da kayan abincin da take yi ga talakawa domin rage musu radadin mawuyacin halin da ake ciki.

Kayan tallafi Source: Twitter 

“Babu kasar da za ta iya kula da tsananin da ake shiga idan an garkame jama’a, ina sane da mawuyacin halin da ake ciki, musamman ma wadanda sai sun fita suke samun abincin da za su ci. “Kamar yan kasuwa, masu aikin yini, masu sana’ar hannu, da ire irensu, na san cewa sai sun fita suke samun abinci, sai sun yi mu’amala da mutane suke samun abinci, amma duk da haka ba zamu sauya dokar ba.

“A makonni 2 da suka gabata, mun sanar da matakan rage radadi kamar rabon abinci, rabon kudi da kuma daga kafa ga masu biyan basussukan gwamnati, za mu cigaba a kan haka.” Inji shi. A hannu guda, Kwamitin dake yaki da yaduwar Coronavirus a Kaduna ta bayyana cewa akwai yiwuwar samun ninkawar adadin masu dauke da cutar a jahar Kaduna saboda rashin bin doka. Kwamitin ta bayyana sakamakon rashin yi ma dokar ta baci biyayya, adadin masu dauke da cutar a jahar Kaduna za su iya kaiwa 57,000, idan dai ba an tabbatar da dabbaka dokar bane.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Buhari ya ce babu shiga babu fita a Legas da Abuja, amma zasu cigaba da raba kudade "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?