
Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu
Thursday, 16 April 2020
Comment
shugaban rundunar sojin Najeriyan ya yi bikin Easter na musamman tare da dakarun kuma ya yi alkawarin zama tare dasu har sai ya kawar da ta'addanci a yankin. Amma kuma, a ranar Alhamis sai 'yan ta'addan suka gwada kwazonsu ta hanyar kaddamar da hari a sansanin duk da sun san cewa shugaban sojin na nan.
Sun kai harin ne a yayin da shugaban ke tare da manyan hafsoshin sojin kasar nan inda suke tsara yadda za su yi wa 'yan ta'addan kifa daya, kwala. Majiya mai karfi daga sansanin wacce ta ce bata da damar zantawa da manema labarai, ta bayyana yadda mayakan ta'addancin suka iso a motocin yaki. Sun bullo ne daga yankin kudu maso yammacin sansanin sannan suka bude wa sansanin wuta, majiyar tace. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kaiwa sansanin hari amma babu wanda ya rasa ransa. Wasu daga cikin dakarun sojin ne suka samu kananan raunika.
Jaridar The Nation ta gano cewa, Buratai ya umarci sojojin da su bi 'yan ta'addan. "Shugaban rundunar sojin ya yi kira ga sojojin da su duba abinda ya faru a matsayin yunkurin dauke musu hankali a kan kokarinsu. Amma mun yi kokari sosai da muka fatattake su," majiyar tace. Wata majiya daban ta bayyana cewa akwai yuwuwar 'yan ta'addan sun fusata ne da yadda suka ga dakarun na ta kokari don har sun fara aiki a jiya.
"Muna tsammanin cewa aikin da muka fita jiya ne ya fusata 'yan ta'addan. Kun san mun kashe musu mutanensu da muka fita jiya kuma mun kama wasu da ransu," ya sanar. Mukaddashin daraktan hulda da jama'a na rundunar, Kanal Sagir Musa, bai samu bada amsar sakonnin da aka tura masa ba. Ya yi alkawarin kira daga baya.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?