
Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga gwamnatin Najeriya
Saturday, 18 April 2020
Comment
Shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau yana tunanin yada makamai tare da mika kansa ga gwamnatin Najeriya, majiya mai karfi ta sirri daga yankin Arewa maso gabas din kasar nan ta sanar da jaridar The Vanguard. Majiyar ta sanar da jaridar cewa, Shekau ya fada neman hanya mai sauki don mika kanshi ga gwamnatin. Kamar yadda majiyar tace, shugaban Boko Haram din ya fara tuntubar wasu kungiyoyin taimakon kai da kai na kasashen duniya don samun ragwame daga gwamnatin Najeriya.
"Ina tsammanin Boko Haram ta kusa zuwa karshe don Shekau na kokarin mika kansa ga hukumomi a Najeriya. "Ya kagara kuma akwai tabbacin cewa tsananta harin da dakarun kasar nan ke kai musu ne ya kawo hakan,"
majiyar tace. Majiyar ta kara da cewa, a kwanakin nan dai kungiyar Boko Haram din na fuskantar kalubale mai tarin yawa sakamakon saka su gaba da dakarun sojin kasar nan suka yi. Kamar yadda majiyar ta bayyana, Shekau na ganin cewa damarsa na niyyar kubce masa. "Shiryayyun harin da ake ta kaiwa mayakan ta'addancin ne yasa suka rasa wurin gudu balle su tsira.
"Shugaban rundunar sojin Najeriya ya bada umarnin damko masa Shekau da ransa. Shugaban ya koma Borno har sai ya ga karshen ta'addanci. "Akwai alamun kuwa zaman ya je yi don babu wata alama da ke nuna ya shirya barin garin ba tare da ya cimma manufarsa ba,"
majiyar tace. Vanguard ta gano cewa kungiyar Boko Haram ta mika kokon bararta ga wasu kungiyoyin taimakon kai da kai na kasashen ketare don nema mata rangwame wurin gwamnatin Najeriya. Wani ma'aikaci a wata kungiyar taimakon kai da kai wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce Shekau yana ta tura musu sakonni don su taimaka masa wajen neman rangwame wurin gwamnatin Najeriya. Kamar yadda ya bayyana, "Da farko mun yi zaton shirme ne amma da lamarin ya ci gaba, dole yasa muka sanar da cibiyoyin tsaro."KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN๐๐๐ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐๐๐
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga gwamnatin Najeriya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?