
Bill Gates ya gargadi yan Arewa game da tasirin cutar Coronavirus a yankin
Friday, 17 April 2020
Comment

Gidauniyar Bill and Melinda Gates ta bayyana cewa yankin Arewacin Najeriya ta fi ko ina kasancewa cikin hadarin fuskantar yaduwar annobar Coronavirus. Shugaban gidauniyar, Mark Susman ya bayyana haka ga yan jaridu a ranar Alhamis, inda yace Arewa na cikin hadarin saboda rashin sahihin tsarin kiwon lafiya a matakin farko.
“Mun yi aiki sosai a yankin Arewa saboda shi ne yanki mafi talauci a Najeriya, tsarin kiwon lafiya a yankin ya tabarbare gaba daya, shi yasa mata masu haihuwa da kananan yara suka fi mutuwa a yankin. “Kasashen Afirka da dama suna da irin wannan matsalar, don haka muke ganin matsalar rashin tsarin ingantaccen kiwon lafiya a matakin farko zai zamo hanya mafi sauki da zai sanya yankin cikin hadarin yaduwar cutar.” Inji shi.
Bill Gate da Dangote a Kaduna Source: Facebook
A hannu guda, Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta nemi kasashen dake kokarin janye dokar ta bacin da suka sanya don gudun kare yaduwar annobar Coronavirus su cika sharudda guda 7. Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake ganawa da manema labaru.
Sharuddan da shugaban WHO ta gindaya ma kasashe kafin su janye dokar sun hada da:
- Dole ne sai gwamnatoci sun tabbata sun dakile yaduwar cutar
- Dole ne sai kasashe sun killace duk wani mai dauke da cutar, tare da musu gwaji
- Dole sai kasashe sun binciko duk wadanda suka yi mu’amala da masu cutar
- Dole kasashe su samar da asibitoci a wuraren da annobar ta fi kamari don kiyaye dawowarta a gaba
- Dole kasashe su samar da matakan kare kariya a wuraren aiki, da makarantu
- Dole kasashe su killace tantance matafi daga kasashen waje don kare shigar cutar kasarsu
- Dole kasashe su wayar da kawunan jama’ansu tare da ilimantarsu game da illar cutarKARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN๐๐๐ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐๐๐
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Bill Gates ya gargadi yan Arewa game da tasirin cutar Coronavirus a yankin "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?