
Bayan cutar Korona ta kashe mahaifin, bata-gari sun soka wa dansa wuka har lahira
Tuesday, 28 April 2020
Comment
Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, ya bar gidan lafiya kalau ba tare da yin wata muhawara da kowa ba. Jami'an 'yan sandan da ke bincike a kan mutuwar matashin mai shekaru 24 sun ce babu wata alama daya da ke nuna fada aka yi da shi har aka kashe shi. Lamarin da yasa har yanzu ba a kama kowa ba. Bayan kammala karatunsa daga jami'ar Southbank a fannin talla, David ya fara aiki da NHS.
A cikin kwanakin nan ne mahaifinsa ya rasu sakamakon cutar coronavirus. Dan sanda mai bincike, Tony Kirk ya ce: "Yan uwan David na fuskantar matukar bacin rai. A cikin kwanakin nan ne suka rasa mahaifinsa sakamakon annobar COVID-19."
David matashi ne wanda ya ke aiki don samun biyan kudin makarantarsa har ya samu ya kammala. Mahaifiyarsa na aiki a NHS ne inda shima ya samu gurbi. "Har a halin yanzu, mun yarda cewa wasu mutane ne suka tare David inda suka sossoka masa wuka har ya mutu," yace. Ya kara da cewa, "Babu shakka shiryawa aka yi don halaka David, don shi kadai aka tare. "David da mahaifiyarsa wadanda suka bada gudumawa mai yawa a yankin, suna bukatar taimakonku.
A halin yanzu suna bukatar duk wanda ya san wani abu game da mutuwar David, da ya garzayo." 'Yan sandan sun gano cewa makasan David sun bar wurin ne a wata mota kirar Silver Dodge Caliber wacce aka bari a kan titin Lincoln da ke Plaistow. An saci motar ne a Dagenham a ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilu.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Bayan cutar Korona ta kashe mahaifin, bata-gari sun soka wa dansa wuka har lahira"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?