
Babbar magana: Saurayi ya kashe dan uwanshi bayan ya kamashi yana zina da uwar da ta haifesu
Saturday, 18 April 2020
Comment
Jami’an hukumar ‘yan sanda na kasar Kenya sun kama wani saurayi mai shekaru 36 da ya fito daga kauyen Bokisero-Nyabwari dake yankin kudancin kasar.
Sun kama saurayin da laifin kashe kaninshi wanda ya bayyana cewa ya kama shi yana zina da mahaifiyar da ta tsugunna ta haifesu a daren ranar Alhamis.
Mutumin mai suna Evans Mamboleo Nyachuba ya ziyaci mahaifiyarsu da misalin karfe 8:30 na dare inda ya kama kaninshi mai shekaru 31 mai suna Fred Onsongo Nyachuba yana zina da mahaifiyarsu mai shekaru 55 mai suna Doria Moraa Nyachuba.
An ruwaito cewa ya bugawa dan uwan nashi falanki a fuska da kanshi, inda ya mutu a take a wajen.
Shugaban hukumar ‘yan sanda na Bokisaba, Philip Masenge, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce yanzu haka ana tsare da Mamboleo a ofishin ‘yan sanda na Ekerenyo.
Haka kuma an kai gawar dan uwan nashi zuwa asibitin Nyamira.
Haka kuma ‘yan sanda sun fara gabatar da bincike akan lamarin.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Babbar magana: Saurayi ya kashe dan uwanshi bayan ya kamashi yana zina da uwar da ta haifesu"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?