--
Ba zan rufe fuskata da takunkumi ba - Trump ya bayyana dalilansa

Ba zan rufe fuskata da takunkumi ba - Trump ya bayyana dalilansa




A ranar Asabar ne shugaban kasar Amurka, Donad Trump, ya bayyana cewa ba zai iya rufe fuska da takunkumi ba duk da sabuwar dokar kare lafiya a kasar Amurka ta bawa 'yan kasar shawarar amfani da takunkumin domin kare kansu daga kamuwa da kwayar cutar covid-19. 


A cewar shugaba Trump, "ba zan iya saka wani takunkumi a fuskata ba, ba zan iya karbar manyan baki har mu gaisa ba a yayin da fuskata ke rufe ba." Trump ya bayyana cewa ba dole bane sai mutum ya bi shawarar da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ta bayar ba a kan amfani da takunkumin fuska. 


"Ba dole bane sai mutum ya saka, bana jin cewa zai iya saka wani takunkumi a fuskata," a cewar Trump. 

Donald Trump Source: Getty Images 


Ya zuwa yanzu, kasar Amurka ta tabbatar da cewa mutane 278,458 sun kamu da kwayar cutar covid-19 a kasar sannan cutar ta hallaka mutum 7000, a cewar kididdigar jami'ar 'Johns Hopkins'. 

New York ce jihar da ta fi fuskantar barazana daga cutar covid-19 a kasar Amurka, kuma tuni gwamnan jihar, Andrew Cuomo, ya fara neman taimakon sauran sassan kasar Amurka bayan cutar ta kashe mutane kusan 3000 a jihar. 



LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ba zan rufe fuskata da takunkumi ba - Trump ya bayyana dalilansa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?