--
An samu bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo - WHO

An samu bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo - WHO

An gano wani dauke da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, lamarin da ya tayar hankulan jama'a a yayin da ake fama da annobar coronavirus. Cibiyar lafiya ta duniya ta ce an tabbatar da samun mai cutar a wani birni mai suna Beni da ke gabashin jamhuriyar Congo. Kamar yadda rahoton ya bayyana, mai dauke da cutar ya mutu ne a safiyar Alhamis a asibiti bayan ya nuna alamun cutar na kwanaki masu yawa. Tabbatar da sam

Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, an sanar da hakan ne a yau Juma'a bayan mutuwar mai cutar a ranar Alhamis. Baya ga barkewar Ebola, jamhuriyar Congo na fama da annobar coronavirus, kyanda da kuma cutar amai da gudawa wacce ta kashe dubban yara.

Mutane 215 ne suka kamu da cutar coronavirus a kasar. Mutane 20 suka rasa rayukansu yayin da 13 suka warke daga cutar. Cibiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayyana Ebola a matsayin annoba tun bayan da cutar ta barke a 2019. Ta taba biranen Goma da wasu kasashe masu makwabtaka. Har zuwa Juma'a,

ba a samu wani wanda ya kamu da cutar ba tun daga ranar 17 ga watan Fabrairu. "Binciken farko ya bayyana cewa mamacin mai shekaru 26 dan asalin yankin Beni ne," takardar kwamitin martanin gaggawa ta sanar. "Kungiyarmu tare da hadin guiwar cibiyar kiwon lafiya ta duniya ta fara zurfafa bincike don aiwatar da matakan kiwon lafiya," ta kara da cewa.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An samu bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo - WHO"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?