--
An samar da wurin gwajin cutar korona a Sokoto da Zaria

An samar da wurin gwajin cutar korona a Sokoto da Zaria





Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta sanar da karin wuraren gwajin cutar korona guda biyu a Najeriya.


A sanarwar da ta wallafa a Twitter, hukumar ta ce za a iya gwajin cutar a asibitin koyarwa na Jami'ar Usman Danfodio a Sokoto da kuma asibitin koyarwa na Jami'r ahmadu Bello da ke Zaria.


Hukumar ta ce yanzu tana da cibiyoyin gwajin cutar korona 15.



 Awani Labarin Kuma: Adadin wadanda suka mutu a Birtaniya ya wuce 20,000




Sashen kula da jama'a na Birtaniya ya ce wasu mutum 813 sun mutu a asibitocin kasar sakamakon cutar korona.
Yanzu jumillar adadin ya zama 20,319 - wannan ya sa Birtaniya ta zama kasa ta biyar da take da fiye da mutum 20,000 da suka rasa rayukansu, tare da Italiya da Spaniya da Faransa da Amurka.




KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Related Posts

0 Response to "An samar da wurin gwajin cutar korona a Sokoto da Zaria"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?