
An rasa wanda zai dauki alhakin dauke gawar da aka wayi gari da ganinta a gefen titi a Kano
Sunday, 26 April 2020
Comment
Majiyar ta bayyana cewa jama'a sun fara taruwa a kan gawar mutumin da misalin karfe 11 na safiyar ranar Asabar bayan sun tabbatar da cewa ya mutu. Ya kara da cewa sun tuntubi jami'an gwamnati tare da sanar da su batun ganin gawar mutumin da basu san ko waye ba. A cewar mutumin, "jami'an hukumar kwana - kwana na Bacirawa muka fara tuntuba amma sai suka ce yankin ba a karkashin kulawarsu yake ba."
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano ya shaidawa BBC cewa sun samu labarin ganin gawar amma ya ce kula da gawa hakkin jami'an lafiya ne, ba 'yan sanda ba. Kazalika, mazauna unguwar sun bayyana cewa sun sanar da ofishin 'yan sanda na Dala, amma sai suka shaida musu cewa su tuntubi ma'ikatar lafiya. "Duk lambobin hukumar NCDC da muka kira babu wacce ta shiga," a cewar Benjamin, wani mazaunin yankin a hirarsa da BBC.
Benjamin ya ce sun sanar da mai unguwar Dala, sannan sun je asibitin Murtla amma babu wanda ya yi wani abu a kan gawar. A cewarsa, gawar ta kai har karfe 12:30 na ranar Asabar amma babu wasu jami'ai da suka zo wurin. Legit.ng ta wallafa rahotanni a kan yadda jama'ar Kano ke zaune cikin zulumi sakamakon yawaitar mutuwar mutane, yawancinsu dattijai.
Jama'a na cigaba da kiraye - kiraye a kan gwamnati ta gudanar da bincike a kan yawaitar mace - macen da ake samu a jihar Kano. Babu wata hujja da ta nuna cewa mutanen da ke mutuwa sun kamu da kwayar cutar covid-19 duk da annobar ta bulla jihar Kano.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "An rasa wanda zai dauki alhakin dauke gawar da aka wayi gari da ganinta a gefen titi a Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?