
An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili
Thursday, 2 April 2020
Comment
matasan sun kuma kona motar bus mallakar Emmanuel Ukandu da ake zargin da ita ya kashe kansilar. Lamarin ya faru ne a garin Umunna, Umuchukwu a karamar hukumar Orumba ta Kudu na jihar ta Anambra.
An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili Source: UGC
An gano cewa Ukandu wanda suka samu rashin jituwa da mammacin saboda fili ya yi amfani da motarsa ne ya nike shi duk da gargadin da yaron motarsa ya masa kan afkuwar hakan.
Mai magana da yawun rundunar tsaro ta NSCDC a jihar, Edwin Okadigbo ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin. Ya ce an sanar da ofishin NSCDC na Orumba ta Kudu afuwar lamarin a ranar Laraba. Okadigbo ya ce, "Binciken da muka gudanar kawo yanzu ya nuna cewa wanda ake zargin ya dade yana rikici da mutane kan mallakin wata fili kuma yana jin haushin duk wadanda ba su goyon bayansa.
"Garin haka ne ya kashe mammacin wanda shine kansila mai wakiltan Umuchukwu a karamar hukumar Orumba ta Kudu, har yaron motarsa ma ya yi ta faɗa masa cewa idan bai dakatar da motarsa ba zai buge mutumin."
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
0 Response to "An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?