--
An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa

An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa



Rundunar yan sanda na jihar Jigawa ta kama wani mutum da aka zargin ya yi matarsa fyade har sai da ta mutu a kauyen Kankaleru da ke karamar hukumar Ringim na jihar. A sanarwar da ya fitar a ranar Jumaa, Mai magana da yawun rundunar a jihar, Abdu Jinjiri ya tabbatar wa Channels Television kama mutumin. A cewar Jinjiri, wanda ake zargin, Alasan Audu ya aikata laifin ne bayan ta ki amincewa su yi kwanciya ta aure.

Kakakin yan sandan ya yi bayanin cewa an tilastawa matashiyar mai shekaru 17 auren mutumin ne mai shekaru 3O. Lamarin ya faru ne kwanaki 2O bayan daura musu aure. Wani sashi na sanarwar ta ce, "Bincike ya nuna cewa misalin karfe 4 na asuba, wanda ake zargin ya kusanci (marigayiyar) a matsayinsa na mijin ta amma ta ki amincewa ya biya bukatarsa tunda dama ba shi ta ke son a aura mata ba da farko.

"Ana zargin a hakan ne ya yi amfani da karfi da yaji ya biya bukatarsa."

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?