
An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani
Monday, 13 April 2020
Comment
- Gwamnatin jahar Kano ta yi feshin magani a wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a jahar - Kwamishinan Muhalli na jahar, Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya jagoranci ma'aikatansa wurin yin feshin
- An dai yi feshin ne a wurare biyar da aka tabbatar ya ziyarta kafin a gane yana dauke da cutar Gwamnatin jahar Kano ta yi feshin magani a wurare biyar da mutumin da aka tabbatar yana dauke da coronavirus ya ziyarta kafin a gano yana dauke da cutar. Kwamishinan Muhalli na jahar, Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya jagoranci ma'aikatansa wurin yin feshin,
shashin Hausa na BBC ta ruwaito. An tattaro cewa an yi feshin ne a Masallacin Juma'a na Da’awah da Masallacin Juma'a na Dan Adalan Kano da cibiyar gwajin cututtuka ta Providian Diagonistic.
Sauran wuraren da aka yi feshin sun hada da cibiyar FAN Diagonistic, da asibitin Prime Specialist da kuma gidan mutumin.
An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani Source: Twitter
Kwamishinan ya jadadda cewar an kulle dukkan wuraren, sannan kuma cewa gwamnati za ta ci gaba da yi musu feshi.
Ku tuna cewa a ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu, ne aka sanar da batun samun mutum na farko da ya kamu da cutar a jahar Kano. An dai rahoto cewa mutumin, wanda ke zaune a karamar hukumar Tarauni, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajiberen ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.
A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jihar tare da tsananta dokar hana shiga da fice a kan iyakokinta. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon bullar muguwar cutar coronavirus a jihar a ranar Asabar. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa BBC cewa tuni aka killace wanda aka samu da cutar a asibitin Pfizer na kwanar Dawaki. Dan shekaru 75 din da haihuwa na nan a killace don hana yaduwar cutar a jihar.
KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN๐๐๐ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐๐๐
LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?