--
An bindige, Charles Tambe, mai tsaron gidan Abia Warriors a Ibadan

An bindige, Charles Tambe, mai tsaron gidan Abia Warriors a Ibadan

Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun harbi mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors, Charles Tambe a birnin Ibadan da ke jihar Oyo kamar yadda Legit.ng ta ruwaito. An gano cewa an garzaya da Tambe zuwa asibiti mai suna University College Hospital (UCH) da ke Ibadan domin samun kulawan likitoci. Kungiyar ta Abia Warrior, a shafinta na Twitter,

@AbiaWarriors ta wallafa afkuwar labaran mara dadin ji inda ta ce: "Wasu 'yan daba sun harbi mai tsaron gidan kungiyar mu, Charles Tambe a safiyar yau a Ibadan. Tambe yana asibiti a UCH a Ibadan yana samun kulawa. Mahukuntan kungiyar mu suna bin dididgin abinda ya yi sanadin afkuwar lamarin. Za mu cigaba da yi muku bayanin abinda ke faruwa. Muna bawa kowa shawarar ya guji afkawa cikin fitina."



A halin yanzu dai babu cikakken bayani a kan abinda ke faruwa a gasar Premier ta Najeriya da ya haifar da hakan a lokacin da ake rubuta wannan rahoton. Ku cigaba da kasancewa da mu domin samun cikakken rahoton ....
LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "An bindige, Charles Tambe, mai tsaron gidan Abia Warriors a Ibadan"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?