--
Yanzu yanzu: Atiku ya yi martani a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa abba kyari

Yanzu yanzu: Atiku ya yi martani a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa abba kyari

- Atiku Abubakar ya yi martani a kan mutuwar Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Buhari - Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce ya kadu da mutuwar Kyari - Atiku wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2019,

ya yi addu’an Allah ya yafe ma Kyari zunubansa sannan ya bashi Aljannah Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya mika ta’aziyyarsa a kan mutuwar Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari. Fadar shugaban kasa ta sanar da mutuwar Kyari a safiyar ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu. Marigayin ya kamu da cutar COVID-19 sannan kuma yana ta samun kulawar likitoci a wani wuri da ba a bayyana ba.

Abba Kyari: Atiku ya yi martani a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa Source: UGC

 Sai dai kuma, ya rasu a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu, kamar yadda sanarwa daga kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya nuna.

Da yake martani, Atiku wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, a zaben 2019, ya bayyana a shafin Twitter: "Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un. Na yi bakin ciki da mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Abba Kyari. Allah SWT ya ba iyalansa hakuri, Allah ya ji kansa ya yafe masa kura-kuransa, ya saka masa da Aljannah Firdaus. Ameen.” Labarin yadda ya kamu da cutar ta Coronavirus dai ya fito ne a watan Maris, inda bayan kamuwarshi da cutar, shi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari aka yi masa gwaji ba a samu cutar a jikinshi ba. Shugaba Buhari, Yemi Osinbajo,

gwamnoni da ministoci da dama sun hadu da shi kafin a gabatar da gwajin cutar a jikinshi. Kyari wanda ya dawo Najeriya daga wata tafiya da yayi zuwa kasar Jamus, a ranar 14 ga watan Maris, ya gana da manyan mutane na Najeriya da dama. Abba Kyari daga baya ya fito ya bayyana cewa za a kai shi birnin Legas daga Abuja domin ya cigaba da karbar magani.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/





LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu yanzu: Atiku ya yi martani a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa abba kyari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?